UMARNIN  BUHARI NA A SANYA IDO KAN WASU MUTANE 50 YA YI DAIDAI – PASALI  

  0
  907

  Isah Ahmed, Jos

  Tattaunawa ta musamman tare da SHUGABAN kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa Muhammad Buhari ta Buhari Campaign Organization na kasa Alhaji Danladi Garba Pasali wanda ya zanta da wakilinmu ya bayyana ra’ayin sad a cewa umarnin da shugaban kasa Muhammad Buhari ya baiwa jami’an tsaron kasar nan, kan su sanya ido kan wasu mutane 50 da ake zargi da handame kudaden Najeriya, don ganin basu fice daga cikin kasar nan ba, ya yi daidai.

   Har’ila yau ya bayyana cewa takarar shugabancin kasar nan, da za ayi a wannan zabe mai zuwa, tsakanin shugaba Buhari da Atiku Abubakar takara ce za ayi tsakanin gaskiya da karya.

   Ga yadda tattaunawar ta kasance

   GTK; Maye zaka ce kan sunaye mutane 50 da gwamnati ta baiwa jami’an tsaro umarnin su  sanya ido a kansu don ganin basu fice daga kasar nan ba?

  Pasali; Wannan mataki da gwamnatin Nijeriya ta dauka yana daga cikin abubuwan da duk wani mai kishin Najeriya  yake son ganin shugaba Buhari ya yi. Domin ‘yan Najeriya sun zabi shugaba Buhari ne domin ya duba wadannan matsaloli. Domin  cin hanci  da rashawa ne ya jefa kasar nan cikin mummunan halin da take ciki. Ya kashe kasar nan ya kawo rigingimu iri iri, ya haifar da ‘yan fashi da makami  da ‘yan tawaye da rashin adalci da rashin kirki  da kwashe dukiyar kasar nan.

  Kuma idan ka tuna Shugaba Buhari ya sha fadin cewa, shi yazo ne  domin ya yi gyara kan wannan matsala ta cin haci da rashawa.

  Kowa yasan Buhari  ba mai dibar dukiyar jama’a bane, domin duk da ya yi minista da gwamna da shugaban kasa, amma kowa ya shede shi bai ci kayan kowa ba. Don haka aka nada shi  shugaban masu yaqi da cin hanci da rashawa na Afrika gabaki daya.

  Saboda haka wannan oda da shugaba Buhari ya kawo dama doka ce da take cikin kundin tsarin mulkin kasar nan.  Domin idan ka tuni watanni 6 da suka gabata ne aka fito da wannan doka. Mutane suka yi ca aka sami wadansu suka tafi kotu.

  Yau ga baki daya bai fi kwanaki uku ba, shugaba Buhari ya kaddamar da wannan doka. Bayan  da kotu ta tabbatar masa da wannan izini. Dama akwai mutane da suke da shari’o’i a gaban kotuna da hukumomin EFCC da ICPC. Haka kuma akwai mutanen da ake zargi cewa sun rarumi dukiyar kasa, a Najeriya.

  A kasashe kamar irin su kasar Ghana kowa yaga irin yadda tsohon shugaban qasar Rowling   ya jera  wadanda suka sace kudaden kasar ya kashe su. A qasar China kashe duk wanda aka samu da laifin cin hanci da rashawa ake yi.

  Ai a Najeriya shugaba Buhari ya yi adalci, da ya ce a zubawa wadanda ake zargi da cin hanci da rashawa ido ne, don kada su fice daga  kasar nan, saboda suna karkashin bincike. Don haka ni banga wani abin damuwa ba, kan wannan al’amari.

  GTK; Wadansu suna zargin  cewa  gwamnati Buhari ta dauki wannan mataki ne don ganin zaben shekara ta 2019 ya gabato.

  Pasali; Ai shi ne nace maka fiye da wata 6 ke nan da kafa wannan doka. Bayan kafa wannan doka wasu suka tafi kotu, don haka ni banga wani laifi ba, kan wannan mataki da shugaba Buhari ya dauka.

  Kuma duk wanda ya san Buhari tun a lokacin yakin neman zabensa  ya fadi cewa zai yaki cin hanci da rasha a kasar nan.

  Martaba shi da ake yi a kasashen duniya ana yin haka ne saboda wannan dalili na yaki da cin hanci da rashawa da yake yi. Domin duniya ta yarda   shi ba barawo bane kuma ba azalumi bane.

  Bari na baka wani misali duk dan Najeriya da ya yaje Saudiya ko Ingila ko Amerika duk inda aka yi cinikin da ya kai dala dubu 10, sai an binciki mutumin da ya yi wannan ciniki. Ko mota mai kyau aka ganka da ita kana yawo, sai an bincike ka.

  Kuma idan ka duba a shari’ar da aka yi a kwanakin baya mutanen da aka fara daurewa  kan cin hanci da rashawa a kasar nan  ‘yan jam’iyyar APC ne, wato tsohon gwamnan jihar Filato Joshua Dariye da tsohon gwamnan jihar Taraba Jolly Iyame. Don haka duk wani mai hankali da ya san Shugaba Buhari  yana yin wannan yaki ne, saboda dalilin da yasa ya fito takarar shugabancin kasar nan ke nan.

  GTK; To yanzu gashi jam’iyyar PDP ta tsayar da tsohon mataimakin shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugabancin kasar nan, baka ganin zai iya kayar da shugaba Buhari a wannan zabe da za ayi?

   Pasali;  Abin da nake son ka gane  mu murna muke yi da jam’iyyar PDP ta tsayar da Atiku Abubakar, saboda mun san an kawo mana wanda zamu yi masa mummunan kaye ne a wannan zabe  da za a gudanar.

  Saboda ina son na tabbatar maka cewa Atiku Abubakar mutum ne da ya yi shekara 8 yana mataimakin shugaban kasa a Najeriya. A lokacin suka rika sayar da kadarorin Najeriya sun sayar da kamfanin sadarwa na Naitel da kamfanin jiragen kasa na Najeriya da kamfanin samar da wutar lantarki na NEPA, a takaice  sun sayar da kamfanoni kusan 40. Kuma a yau idan ka tambaye su,  maye suka yi da kudaden da suka sayar da wadannan kamfanoni ba zasu iya gaya maka komai ba. Kuma duk wadannan kamfanoni da suka sayar, kansu suka sayarwa.

  Don haka ina tabbatar maka cewa fitowar Atiku Abubakar a wajen mu mu da muka san waye Atiku mun san garabasa zamu samu.

  Yau idan kaje kauyen Atiku Jada babu wuta babu hanyar mota duk da cewa ya yi shekara 8 yana mataimakin shugaban kasar nan. Yau idan ka tashi daga Gombe a mota kace kana son kaje Yola babban birnin jihar Adamawa wato jihar Atiku,  sai kayi awa 8  tafiyar da bata fi awa 2 ba, saboda rashin kyan hanya.

  Saboda haka mutumin da bai iya gyara kauyensa da jiharsa ba, babu abin da zai yi idan ya zama shugaban Najeriya.

  Wato wannan  wani zabe ne za ayi,  tsakanin gaskiya da karya.  Akwai wanda yake wakiltar dukkan  wasu mutane barayi, macuta azalumai wadanda suka handame dukiyar kasar nan, wakilin wadannan mutane shi ne  Atiku Abubakar. Haka kuma duk wadanda suke da ra’ayin a gyara kasar nan, a kawo cigaba wakilinsu shi ne shugaba Buhari. Kaga babu yadda za ayi, karya ta   kayar da gaskiya.

  GTK; Wanne sako ko kira ne kake da shi  ga al’ummar Najeriya?

   Pasali; Sakon  da nakeshi  ga ‘yan Najeriya shi ne lokaci ya zo da zasu baiwa shugaban kasa Muhammad Buhari goyan baya a wannan zabe mai zuwa. Al’ummar Najeriya su tabbatar sun dawo da shugaba Buhari kan shugabancin kasar nan don a sami adalci, a sake samun cigaba a kasar nan.

  Kowa ya san cewa hawan Buhari mulkin kasar nan shekaru 3 da rabi  da suka gabata, ya sake farfado da jiragen kasa a Nijeriya. Hanyoyin da ada basu da gyara yanzu ya gyara su. Ga aikin wutar lantarki na Mambila a jihar Taraba da sake farfado da kamfanin mulmula karafa na Ajakuta.

  Ga farfado da aikin gona a kasar nan, yau mutanen Najeriya babu ruwansu da maganar sayo shinkafa daga waje, yanzu ana fitar da kayayyakin amfanin gonar da aka noma a Najeriya zuwa kasashen waje. Ga maganar tsaro,  ada kowa  tsoron shiga masallaci ko coci ko kasuwa da tashoshin mota yake yi a Najeriya, saboda tsoron tashin bam. Don haka zaben shugaba Buhari da al’ummar Najeriya suka yi alheri ne ya kawowa kasar nan.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here