Za\’a Fara Neman Mai Da Iskar Gas A Arewa, Ana Son Rage Dogaro Da Neja Delta

0
536

Daga Usman Nasidi

KARAMIN ministan mai na kasa, Mista Ibe Kachikwu, a gefen taron da ake a Abuja, na Nigerian Gas Association 11th International Conference and Exhibition, yace gwamnatin Tarayya na kokarin fara neman iskar gas a wajen Neja Delta.

A cewar wakilinsa, kuma mai bashi shawara a kan upstream and gas, Gbite Adeniji, a arewa za\’a fara nema da haqar iskar ta Gas mai kyaun makamashi wanda yafi na fetur tsafta da kima.

A kasuwannin duniiya ma yafi tsada, sai dai cirarsa ma akwai wahala, domin kamar bam yake, cike da qarfi.

za\’a kuma haqa bututai da zasu tashi daga Ajaokuta zuwa Kaduna sannan su qarasa Kano, a wani shiri da ake kira da AKK gas pipeline project, wanda zai ci maqudan biliyyoyin daloli.

A baya ma dai, gwamantoci na soji da na siyasa, sun so suyi irin wannan babban aiki, sai dai ko lokacin wa\’adin mulki, kko na rayuwa ya hana su, musamman ganin yadda ake tata-burza da \’yan yankin da ake haqar arzikin, da gori da suke wa saura, da ma kuma kokarin sanya arewar ita ma a turbar dogaro da kanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here