Sanata Shehu Sani Yayi Tir Da Kashen Bayin Allah Da Aka Yi A Kaduna

0
481

Daga Usman Nasidi

FITACCEN ‘Dan Majalisar Dattawan nan Sanata Shehu Sani yayi Allah-wadai da kisan da ake yi a kasar nan ba tare da alhaki ba. Sanatan na APC ya nemi a kawo karshen wannan musiba.

A kwanan nan ne aka kashe wasu Jami’an tsaro na ‘Yan Sanda har 2 da kuma wani Bawan Allah guda a Jihar Kaduna.

‘Yan bingida ne dai kurum su ka far masu wanda Sanatan yace dole a gano wadanda su kayi wannan aiki.

Hakan na zuwa ne jim kadan bayan wani ‘Dan Sanda ya harbe wata Budurwa mai suna Anita Akapson har lahira.

Sanatan ya tofa albarkacin bakin sa inda yace dole a kawo karshen wannan mugun aiki da Jami’an tsaro su ke yi.

Marigayiya Anita Akapson ba ta dade da dawowa Najeriya ba inda ta ke aiki da Gwamnatin Tarayya ta sai ta gamu da ajalin ta wajen wani ‘Dan Sanda.

Sanatan dai ya aikawa Iyalan wannan Marigayayi da ke Kaduna da ta’aziyar sa. Idan ba ku manta ba a cikin makon nan ne kuma ‘Yan ta’addan Boko Haram su ka kashe wata Malamar lafiya mai suna Hauwa Liman.

‘Dan Majalisan dai yayi amfani da shafin sa na Tuwita wajen jimamin wannan abin takaici a Kasar.

Yanzu dai ana bincike game da lamarin amma Sanatan na APC da ke wakiltar Yankin Jihar Kaduna ta tsakiya yayi amfani da shafin sa na Tuwita inda yace dole Jami’an tsaro su daina wuce gona da iri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here