Shugaba Buhari Ya Karbi Bakuncin Jaruman Fina-Finan Hausa Maza Da Mata

0
469

Daga Usman Nasidi

A DAREN ranar Alhamis, 18 ga watan Oktoba, ne jaruman masana\’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood su ka ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar sa dake birnin tarayya, Abuja.

Jaruman masana\’antar shirya fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood sun cika da murna da farinciki a yayin da su ka ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar sa domin nuna goyon bayansu gare shi.

Akwai annashuwa da fara\’a a fuskokin jaruman, maza da mata, a hotunan da su ka dauka da shugaba Buhari yayin ziya.

Masana\’antar Kannywood ta dade tana bawa shugaba Buhari goyon baya, don ko a shekarar 2015 bayan Buhari ya lashe zabe, kafin a rantsar da shi, sai da jaruman masana\’antar ta Kannywood su ka kai masa ziyara a gidansa da ke Daura.

Daga cikin jarumana da su ka kaiwa shugaba Buhari wannan ziyara akwai; Hamisu Lamido (Iyantama), Daushe, Nura Hussain (Ya sayyadi), Rukayya Dawayya, Fati Nijar, Sadiq M. Sadiq, Aminu Saira, Rabi\’u Rikadawa, Fati Shu\’uma da wasu da dama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here