Yan Bindiga Sun Sace Wani Babban Basarake Da Matar Sa A Jihar Kaduna

0
481

Daga Usman Nasidi

LABARIN da muke samu da dumin sa na nuni ne da cewa wasu \’yan bindiga da ba\’a san ko suwa ye ba sun sace babban basaraken nan na al\’ummar Adara, watau Agwon Adara mai suna Mai Martaba Maiwada Galadima III ranar Juma\’a.

Mun samu cewa dai an sace basaraken ne tare da matar sa yayin da suke kan hanyar su ta zuwa Kachia daga garin Kaduna, babban birnin jihar cikin motar su.

Rahotanni sun bayyana cewa an dai ga direban motar da Basaraken yake ciki da kuma dogarin sa a cikin motar dukkan su basu cikin hayyacin su yayin da shi kuma basaraken da matar tasa ba\’a gan su ba sama ko kasa.

Jami\’in hulda da jama\’a na rundunar \’yan sandan jihar ta Kaduna dai bai daga waya ba domin yin karin bayani har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

A wani labarin kuma, Shugaban kamfanin nan na yada labarai na Daar Communication, Cif Raymond Dokpesi ya sake jefa tsohon mai ba tsohon shugaban kasar Najeriya shawara ta fuskar tsaron kasa, Sambo Dasuki cikin wata sabuwar cakwakiya a game da batun kudaden nan da suka kai Naira biliyan 2.1 da suka yi batan dabo.

Cif Raymond Dokpesi da yake bayani a gaban alkali a kotu inda ake tuhumar sa da handame kudin, ya bayyana cewa Sambo Dasuki din ne ya ba kamfanin nasu kudin a matsayin kudin aikin da suke yi don haka shi bai da laifi ko kadan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here