Zaben 2019: Manjo Al-Mustapha Yayi Wa Shugaba Buhari Wankin Babban Bargo

0
492

Daga Usman Nasidi

TSOHON dogari ga tsohon shugaban kasar Najeriya Marigayi Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha yayi alkawarin maido da kasar nan akan turba madaidaiciya idan dai har aka zabe shi shugaban kasa a zaben 2019.

Manjo Al-Mustapha da ke zaman dan takarar shugaban kasa a jam\’iyyar PPN ya shaidawa manema labarai a garin Abuja cewar idan har ya zama shugaban kasa to tabbas zai yi kokari wajen ganin ya gyara tabarbarewar da harkokin sukayi a wannan mulkin na Shugaba Buhari.

Haka zalika ya bayyana cewa yan kasar sun cancanci kyakkyawan shugabanci a dukkan matakai shi yasa ma ya ga ya dace ya fito takarar domin ya cece su daga kangin mugun shugabancin da suke ciki.

Da yake bayani game da dan takarar, shugaban jam\’iyyar ta PPN, Honorabul Eyiowuawi Razak ya kwatanta Manjo Al-Mustapha a matsayin babban mai kishin kasa da ya sadaukar da rayuwar sa wajen cigaban ta.

A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya shaidawa manema labarai cewa mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya bashi tabbacin cewa gwamnatin tarayya bata da shirin sayar da kamfanin nan na mulmula karafa na Ajaokuta da ke a jihar ta Kogi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here