SHUGABAN TURKIYYA ERDOGAN ZAI TONA ASIRI GOBE TALATA

0
592

Mustapha Imrana Abdullahi

SHUGABAN kasar Turkiyya Erdogan ya shaidawa duniya cewa a gobe Talata ne ya shirya fayyacewa duniya irin yadda aka Kashe Dan jaridar kasar Saudiyya a cikin ofishin jaladancin Saudiyya da ke kasarsa.

Shi dai Dan Jarida Jamal Khashoggi kamar yadda rahotanni suka bayyana yaje ofishin jakadancin Saudiyya ne da ke Turkiyya domin Neman takardar shaidar aure kamar yadda yake kunshe a cikin tsarin kasar Saudiyya

Amma Sai dai bayan an dauki tsawon lokacin wadda suka je ofishin tare tana Kiran fitowarsa bata ga komai ba duk da an dauki tsawon lokaci.

Hakika bacewar Dan Jarida Jamal Khashoggi ya haifar wa kasar Saudiyya matsalolin jakadanci tsakanin ta da sauransu kasashen duniya musamman a kan huldar Kasuwa ci India wadansu jihohin ma suke janye daga yarjeneniyar harkar sayar wa da Saudiyya makamai wasu kuma suka janye daga batun yarjeneniyar Kasuwa ci da dai sauransu da dama.

Shi dai wannan Dan Jarida Jamal Khashoggi ya yi batan Dabo ne tun ranar Biyu ga watan da ya gabata, inda aka yi ta takaddamar inda yake Sai da matsin lamba ta yi wa kasar Saudiyya sannan ta bayyana cewa tuni wasu sun Kashe shi a cikin ofishin jakadancin Saudiyya da ke Istanbul babban birnin kasar Turkiyya.

Kamar yadda rahotanni suke fitowa sun Nuna cewa shi dai Khashoggi na yawan yin rubutun da baya yi wa kasar Saudiyya dadi wanda yasa shi yin suna a duniya musamman ga masu karanta rubuce rubucen nasa a duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here