Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
HUKUMAR bayar da agajin gaggawa ta Jihar Kaduna SEMA ta bayyana cewa mutane 23 ne suka rasa rayukan su yayin da wadansu mutane 17 sakamakon irin abin da ya faru a cikin garin kaduna a ranar Lahadin da ta gabata.
Babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Kaduna, SEMA Mista Ben Kure ne ya bayyana hakan a ranar Litinin Jim kadan bayan shi da tawagarsa sun dawo daga ziyarar Gani da Ido a yankunan da abin ya faru
Ben Kure, ya yi kira ga daukacin al\’umma da su zauna lafiya su kiyayi tashin hankali.
Ya ci gaba da bayanin cewa babu wata al\’umma da za ta ci gaba a cikin halin rashin zaman lafiya
Sakataren hukumar ya kuma jajantawa wadanda lamarin ya shafa da wadanda suka samu Raunuka India ya kuma Mika sakon ta aziyyarsa da mamatan sakamakon tashin tashinar.
Ya jaddada manufar Gwamnatin Jihar na tabbatar da samun zaman lafiya da tsaron dukiya da rayukan Jama\’a ta harkar samar da tsaro.
Kure ya kuma godewa Gwamna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa\’i bisa irin yadda ya dauki mataki cikin sauri.