AN SHAWARCI GWAMNATIN KADUNA TA SASSAUTA DOKAR HANA FITA

0
573

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

AN Shawarci Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmad El- Rufa\’i ta sassauta dokar hana fitar da ta Saka tsawon sa\’o\’i Ashirin da hudu domin ba dimbin Talakawan da suke da rinjaye damar Neman abin da za su ci.

Wani masanin harkokin yada labarai da ke da  cikakkiyar kwarewa a kan Hulda da kafafen sadarwa Alhaji Ahmed Mai Yaki ne ya yi wannan Kiran cikin wata takardar da ya aikewa kafafen yada labarai a kaduna.

Alhaji Ahmed Mai Yaki ya ce hakika ya Lura da cewa Mafi yawan jama\’a suna rayuwar hannu baka hannu kwarya ne kasancewar Sai sun fita ne a kullum za su samu abin da za su Saka a bakunansu tare da iyalinsu.

Takardar ta ci gaba da cewa saboda irin matsalar Talauci tare da bambancin da ke tsakanin masu hannu da shuni da yan Allah ya Baku mu samu da rashin dai daiton al\’amura da ya haifar da dimbin matsalar rashin abin yi duk sun taimaka wajen cakudewar al\’amura da dama.

\”Mutane na ciyar da Kansu tare da iyalansu daga irin yan kananan sana\’o\’in da suke yi a kullum wanda Sai sun fita ne za su iya samun na abinci. Mutane ba su da karfin da za su ajiye kayan abinci da yawa a gidajensu saboda ba su da halin yin hakan.Akwai matsanancin Talauci a cikin jama\’a wanda kuma hakan ne babbar barazana ga zaman lafiya\” inji Mai Yaki.

Mai Yaki, ya kuma yi godiya tare da jinjina ga Gwamnatin Jiha da kuma Jami\’an tsaro bisa irin yadda suka dauki mataki cikin sauri tun lokacin da rikici ya faru,ya kuma yi gargadin cewa dokar hana fita ta kasance wani tsari ne na dakatar da jama\’a wajen hana fita, Amma idan lamarin ya yi kamari da yawa zai iya haifar da barazana ga zaman lafiya da al\’amuran tsaro.

Ahmed Mai Yaki, wanda ya kasance tsohon Darakta Janar ne a kan harkokin kafafen yada labarai da kuma yada bayanai na Gwamnatin da ta gabata, ya Shawarci Gwamnatin da ta duba sassauta dokar da a akalla sa\’o\’i Goma sha biyu saboda jama\’a su samu zuwa wuraren ayyukansu domin Neman abin da za su ciyar da iyalansu, \”Da akwai rahotanni da ke bayanin cewa mutane na cikin matsanancin Hali a gidajensu wanda hakan barazana ce ga zaman lafiya da al\’amarin tsaro\”

\” Kuma mafita ga irin wannan Hali shi ne Gwamnatin ta hanzarta daukar matakan da za su kawo sauki ga halin da ake ciki domin gujewa samun karyewar tattalin arziki\”. Inji Mai Yaki kamar yadda ya yi gargadi.

Takardar ta kara da bayar da shawara ga jama\’ar Jihar kan su guji duk wani al\’amarin tashe tashen hankali da tsakanin bambance bambancen addini dana kabila domin samun ci gaban da ake bukata a Jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here