Gasar Karatun Al-Kur\’ani: Dan Asalin Jihar Katsina Ya Bayar Da Mamaki A Saudiyya

0
581

Daga Usman Nasidi

WANI dan asalin jihar Katsina da ya fito daga karamar hukumar Katsina, Abdulganiyu Aliyu ya yi nasarar zuwa na uku a gasar karatun Al-Qurani mai girma na kasa da kasa ta 2018 da akayi a kasar Saudiyya.

Abdulganiyu Aliyu ya fafata a gasar ne tare da sauran mallarta gasar guda 115 daga kasashe 82 na duniya.

Majiayrmu ta samu labarin cewa mai bawa gwamnan jihar Katsina shawara na musamman kan ilimi mai zurfi, Mallam Bishir Usman Ruwan Godiya wadda ya yiwa Aliyu rakiya zuwa wajen gasar.

Abdulganiyu Aliyu da kuma Ameer Yunus daga jihar Bauchi ne suka wakilci Najeriya a wajen gasar da aka gudanar a birnin Madina da ke kasar Saudiyya.

Abdulganiyu Aliyu ya zo na uku a fannin hadar izihi 60 na gasar karatun Al-Qurani yayin da shi kuma Ameer Yunus ya zo na uku a bangaren hadar izihi 60 na Al-Qurani tare da tajawidi.

Kasar Saudiyya mai masaukin baki ita ce ta zo na farko sannan kasar Libiya da Najeriya suke biye da ita.

Wannan dai ba shine karo na farko ba da \’yan Najeriya ke nuna irin wannan bajinta a fagen gasar karatun Al-Qurani mai girma a fadin duniya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here