RIKICIN KADUNA: MATASA SUN KOKA KAN ABIN DA KE FARUWA

0
725

Daga Usman Nasidi

WASU matasa a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya sun koka kan yadda rikici mai nasaba da addini da kabilanci ke haddasa rashin zaman lafiya tsakanin al\’umma.

Matasan na kabilu da addinai daban-daban, sun shaidawa cewa ba sa jin dadin abin da ke faruwa a jihar.

Daya daga cikinsu mai suna Bilkisu Ahmed wadda mabiya addinin kirista ce ta ce \”Kisan da ake yi a jihar Kaduna da ma sauran jihohin Najeriya ba ya mana dadi, a duk lokacin da aka samu rikici irin wannan, wadanda ba su san hawa ba su san sauka ba lamarin ke rutsawa da su, abin da ke faruwa baya mana dadi mu matasa\”.

Ta ce ya kamata a yi karatun ta-natsu, \”wannan abin da ake yi ba ya kawo ma na ci gaba sai dai ci baya\”.

Shi ma wani matashi Awwal Abdallah ya ce bai ga dalilin da yana matashi da jini a jikinsa haka kawai ya ga ana rikicin addini da kabilanci a kuma dauki makami ya far wa mutane.

Awwal ya kara da cewa \’\’Babu yadda za a yi mutum mai ilimi ya dauki makami ya kashe dan uwansa ko dai musulmi ko kirista, wannan ba daidai ba ne\”.

\”Kuma babu inda addinin musulunci ko na kirista ya ce a aikata hakan don wannan abu haramci ne baki daya.\’\’

A karshe matasan sun yi kira ga \’yan uwansu su daina shiga rikicin haka nan kawai, su nesanta kansu da ayyukan tada zaune tsaye.

Sun yi kira ga zaman lafiya tsakanin al\’umma, da kokarin sasanta rikici da sanya jami\’an tsaro a duk lokacin da lamurra suka fara dagulewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here