Isah Ahmed Daga Jos
WANI dan takarar kujerar majalisar dokoki ta Jihar Filato daga mazabar Jos ta Arewa Maso Arewa karkashin jam’iyyar UPP, Malam Majiburrahman S. Musalla ya bayyana cewa gwamnonin Jihohi ne matsalar Najeriya. Majiburrahman S. Musalla ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu.
Ya ce gaskiya gwamnonin Najeriya suna nuna son rai tare da yin karfa karfa a harkokin siyasa da harkokin mulki tare da taka kowa a jihohinsu. Kuma sai wanda suke so yake samun mukamin siyasa ko mukaman wasu harkoki na cigaban jama’a.
‘’ Sakamakon wannan karfa karfa da gwamnoni suke yi ‘yan majalisun Jihohi sun zama ‘yan amshin shatansu, sai abin da gwamnonin suke so suke aiwatarwa. Kuma gwamnonin basa yin wasu ayyuka na cigaba a Jihohinsu ba’’.
Majiburrahman Musalla ya ce ya kamata matasa da sauran al’ummar kasar nan, su tashi don ganin an magance wannan matsala ta gwamnoni a Najeriya.
‘’Dangane da takarar da na fito babban abin da ya karfafa mani gwiwar fitowa wannan takara, shi ne ganin irin wahalar da al’ummar mazaba ta take ciki, ya sanya na fito wannan takara. A halin da ake ciki babu wani abu na cigaba ko kyautata rayuwar al’umma, da ‘yan majalisun wannan mazaba suka yi. Tun daga lokacin da aka dawo mulkin damakoradiya, har ya zuwa wannan lokaci. Idan Allah ya sami na sami nasara, ina da kudurin inganta harkokin kiwon lafiya da ilmi da tallafawa matasa a wannan mazaba’’.