KUN SAN MATAR DA ZA TA ZAMA MATAIMAKIYAR EL-RUFAI?

  0
  896

  Rabo Haladu Daga Kaduna

  GWAMNAN jihar Kaduna Nasir Ahmad El-Rufai ya sanar da zaben Dakta. Hadiza Balarabe a matsayin matar da za ta zame masa mataimakiya a zaben 2019.

  A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Gwamna El-Rufai ya ce ya zabi Dakta Hadiza Balarabe ne domin karfafa gwiwar mata. Dr. Hadiza Balarabe ita ce babbar sakatariya a hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar Kaduna.

  A cewar El-Rufai, manyan ayyukan Dakta Hadiza Balarabe sun hada da kaddamar da shirye- shiryen da suka inganta tsarin kiwon lafiya na jihar ta Kaduna.

  Dakta Hadiza ta soma aiki a fannin lafiya na babban birnin tarayya, Abuja a 2004 inda ta kai matsayin daraktar kula lafiy.

  Gabanin hakan, ta rike mukamin babbar rijistara a asibitin koyarwa na Jam\’iar Ahmadu Bello da ke Zariya.

  Ta karanci aikin likita a Jami\’ar Maiduguri inda ta kammala a shekarar 1988.

  Zaben nata dai ya sha suka a wurin wasu \’yan jihar, musamman \’yan yankin Kudancin Kaduna wadanda ke ganin bai kamata Gwamna El-Rufai ya zabi musulmi ba tun da a al\’adance Kirista ake zaba domin su tafi tare.

  Sai dai wasu sun yaba wa gwamnan bisa yin la\’akari da kwarewa ba siyasa ba a zaben mataimakiyar tasa.

  A cewarsu, babu dalilin da zai sa \’yan Kudancin Kaduna su tayar da hakarkarin wuya kan zaben Dr. Hadiza tun da ita ma \’yar yankin ce.

  A farkon shekarar nan ne dai mataimakin gwamnan jihar Barnabas Yusuf Bala, ya bukaci Gwamna El-Rufai ya ba shi damar sauka daga kan mukamin idan suka kammala wa\’adinsu na farko, yana mai cewa ya fi son tsayawa takarar dan majalisar dattawa.

  Yanzu dai shi jam\’iyyar APC mai mulkin jihar ta tsayar takarar sanata da zai wakilci Kudancin Kaduna a zaben 2019

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here