Isa Ashiru Ya Tabbatar Da Sahihancin Takardunsa Na Makaranta

  0
  503

  Mustapha Imrana Abdullahi

  DAN takarar Gwamnan Jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar PDP, Alhaji Isa Mohammed Ashiru, ya tabbatar da cewa takardunsa na makaranta wadanda ya gabatar ga hukumar zabe ta kasa sahihai ne kuma cikakku.

  Saboda haka ne dan takarar ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar PDP da masu yi masa fatan Alheri da su yi watsi da rade–radin da ake yi cewa takardun nasa nada matsalar da ka iya jawo a dakatar da shi daga yin takarar.

  Ya ce wadannan maganganu marasa tushe sun samo asali ne daga kidimar da jam’iyyar APC mai mulki a jihar ta yi tun zamowar Alhaji Isa Ashiru dan takara saboda haka take bin dukkan hanyoyi don ganin ta cusa shakka da rudani a zuciyoyin jama’ar Jihar Kaduna dangane da takarar tasa.

  Isa Ashiru, ya tunawa masu yada wannan batanci cewa shi fa ya yi takara kuma ya ci zabubbuka har sau hudu a tsakanin shekarar 1999 da ta 2015 kuma sai da ya gabatar da dukkan takardunsa na makaranta kamar yadda doka ta tanada kafin hukumar zabe ta amince masa ya tsaya takarar a wadancan zabubbukan.

  Sannan ya yi tambayoyi kamar haka,Ya ya za a yi na zama dan majalisar Jihar Kaduna daga shekarar 1999 zuwa ta 2007 sannan a sake zabe na har sau biyu a matsayin dan majalisar wakilai ta tarayya daga shekarar 2007 zuwa 2014 idan takarduna nada matsala ko kuma basu cika ba? Ko kuma daga yaushe ne matsalar takardun nawa ta baiyana?

  Dan takarar ya ce ya dai lura wadanda ke yin wannan kame–kame na kokari ne su samu wani abu da zasu fada dazai  dadada musu zuciya musamman tun da sun tabbatar karshen mulkinsu ya zo.

  Alhaji Isa Mohammed Ashiru ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da fafutukar ganin an kwato jihar Kaduna daga hannun shugabanni marasa tausayi da adalci tare kuma da kara yin kira ga dukkan magoya bayansa da su kasance masu juriya da dukkan wani cin mutunci da zasu fuskanta daga jam’iyyar APC da gwamnatinta.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here