Me Ya Sa Kungiyar Malaman Jami’a Ta ASUU Ta Shiga Yajin Aiki?

0
20

 Rabo Haladu Daga Kaduna

KUNGIYAR malaman jami’a ta Najeriya, ASUU ta tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani ranar Litinin.

ASUU ta yanke shawarar shiga yajin aikin ne bayan taron da kwamitin zartarwarta na kasa ya yi a Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke birnin Akure na jihar Ondo ranar Lahadi da almuru.

Kungiyar ta zargi gwamnatin taraya da gaza aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a baya game da yadda za a inganta yanayin aiki a jami’o’in.

Da yake tattaunawa da manema labarai, shugaban kungiyar na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi ya ce dukkan yunkurin da suka yi na gamsar da gwamnatin tarayya don ta mutunta yarjejeniyar ba ta biya bukata ba.

A cewarsa, dukkan jami’o’in tarayya da na jihohi ne za su tsunduma cikin yajin aikin.

Masu sharhi kan ilimi dai sun yi kira ga gwamnati da malaman jami’o’in da suka rika yin sulhu a tsakaninsu ta yadda ba sai an kai ga shiga yajin aiki ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.