NAKASASSUN JIHAR JIGAWA  SUN JINJINAWA GWAMNA BADARU.

0
583

JABIRU A HASSAN, Daga Dutse.

NAKASASSU a jihar Jigawa sun nuna godiyar su bisa yadda gwamnatin jihar take kulawa dasu tareda basu hakkokin su batare da tsaiko ba  hakan ta sanya suke  gudanar da zamantakewa mai kyau kamar kowa.

Wannan tsokaci ya fito ne daga malam Usman   Musa gidan Lage cikin yankin karamar hukumar Ringim a zantawar su da wakilin mu, inda ya nunar da cewa nakasassu a jihar Jigawa sai godiya tsakanin su da gwamnatin Badaru musamman ganin yadda take daukar matakai na kare mutuncin su da kyautata rayuwar su kamar kowane dan jihar.

Yace suna jin dadin yadda ake basu alawus duk wata, sannan sun yarda cewa gwamna Badaru Abubakar shugaba ne mai tausayi da kaunar talakawan sa kamar dai yadda ake gani a halin yanzu, tareda fatan alheri ga gwamnati da dukkanin masu hannu wajen kulawa dasu batare da nuna gajiyawa ba.

Malam Usman Musa wanda akafi sani da (Baba Kwalla), yayi amfani da wannan dama wajen yin roko ga gwamna Badaru da ya duba yiwuwar kara yawan tallafin da ake basu  da kuma kara zakulo nakasassu domin a taimaka masu ta yadda suma zasu amfani wannan shiri na tallafawa nakasassu a jihar Jigawa.

Daga karshe, Usman Gidan Lage ya sanar da cewa nakasassu sun tanadi katunan zabe domin sake dangwalawa gwamna Badaru Abubakar kuri\’u ta yadda zai ci gaba da aiyukan alherin da yake yiwa al\’uma kamar yadda kowa yake gani a halin yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here