YAN BINDIGA SUN KASHE UBA, TARA DA SACE YARSA

0
547

Mustapha Imrana Abdullahi

WADANSU yan Bindiga da suka Kai hari a garin Kankiya sun harbe wani magidanci tare da yin awon gaba da yarsa

Yan bindigar da ba a san Ko su Waye ba a ranar Talatar da ta gabata ne suka harbe har lahira wani Alhaji Nasiru Maimasara, inda daga baya kuma suka Sace yarsa duk kan wannan lamarin ya faru ne a unguwar Gachi a karamar hukumar Kankiya.

Majiyar mu ta shaidawa wakilinmu cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe biyu na Daren ranar Talata.

\”A lokacin da yan bindigar suka Kai harin sun rika yin kuwwa suna ta harbin kan Mai uwa da wabi, yayin da suke matsawa zuwa Gidan Mai Masara a unguwar Gachi\” majiyar da ta nemi a sakaya sunanta.

\”Yan bindigar sun harbe shi ne lokacin da yake kokarin Guduwa,domin ya gudu da marasa.

\”Bayan sun harbe shi an dauke shi zuwa babban asibitin Kankiya inda aka tabbatar da cewa ya fadi\”. Inji majiyar mu.

Kuma tuni aka binne gawarsa yayin da masu kokarin zuwa Gidan domin jaje suke tururuwa Gidan marigayin.

Jami\’an Hulda da jama\’a da ke magana da yawun rundunar yan sandan Jihar Katsina Gambo Isa ya tabbatar da faruwar lamarin.

Isa ya ci gaba da cewa rundunar na kokarin gano wadanda suka aikata lamarin wato yan bindigar.

\”Tuni Mika rigaya muka baza jami\’an tsaro suna nan suna ta aikin binciken lamarin.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here