An Rufe Wata Makaranta A Kudancin Najeriya Saboda Wasu Dalibai Sun Saka Hijab

0
616

Daga Usman Nasidi

SHUGABAN makarantar University of Ibadan International School, Phebean Olowe ya rufe makarantar saboda rashin amincewa dalibai mata musulmi su saka hijabi yayin da za su zo makaranta.

An dai rufe makarantar ne bayan an hango wasu dalibai sanye da hijabi sun nufo makarantar wadda hakan ya saba dokar makarantar kamar yadda mahukunta makarantar suka bayyana.

Wasu iyayen yara karkashin kungiyar iyayen yara musulmai sun aike wa makarantar wasika a ranar 9 ga watan Nuwamba dauke da sa hannun Abdurrhman Balogun (Chairman) da Bilkis Badiru (Secretary) inda suka sanar da mahukuntar makarantar cewar yaransu mata za su fara saka hijabi.

Kungiyar ta bayyana cewar baya ga cewa Ibada ne \’ya\’ya mata su saka hijabi a musulunci, suna da ikon saka hijabin a karkashin dokar Najeriya.

A yayin da ya ke tsokaci kan lamarin, Shugaban kotun makarantar, Farfesa Abideen Aderinto ya bayyana cewar makarantar ba za ta amince da matakin da iyayen suka dauka ba.

Ya ce makarantar ba ta gwamnati bane saboda haka suna da damar kafa dokoki mudin iyayen makaranta sun amince da shi. \”Duk wanda ke son canja wata doka a makarantar sai ya bi ta hanyoyin da suka dace,\” inji Aderinto.

A bangarensa, Balogun ya yi mamakin yadda aka rufe makaranta saboda kawai wasu dalibai mata sun saka hijabi duk da cewa suna da ikon sakawa a karkashin dokar Najeriya.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here