Kotu Ta Yanke Ma Yaron Daya Kashe Babansa Akan Kudi A Bauchi Hukuncin Kisa

0
555

Daga Usman Nasidi

WATA kotun daukaka kara dake zamanta a garin Jos ta sanar da yanke hukuncin kisa akan wani matashi Jibril Idrisa wanda ta kama da laifin halaka mahaifinsa har lahira sakamakon rikicin kudi naira dubu hamsin da shida (N56,000) a jahar Bauchi.

Majiyarmu ta samu labarin cewa Alkalin kotun, Mai sharia Habiba Abima ta yi watsi da hukuncin wata babbar kotun jahar Bauchi da ta wanke matashin daga laifin, sa’annan ta sakeshi a baya.

“Wannan kotun mai adalci ta yi fatali da hukuncin karamar kotu da ta wanke Jibril Idris, sa’annan ta sakeshi, don haka mun kamashi da laifin kai, laifin da yayi karantsaye ga sashi na 211 na kundin hukunta laifuka na jahar Bauchi.

“Don haka Kotu ta yanke ma Jibril Idris hukuncin kisa ta hanyar rataya.” Inji mai sharia Habiba Abimata kotun daukaka kara na jahar Bauchi.

Yan uwa da sauran dangin mamacin ne da kansu suka daukak kara zuwa kotun, inda suke nemi kotun da ta yi watsi da hukuncin Alkali M.A Sambo na babbar kotun jahar Bauchi dake zamanta a garin Bauchi wanda shi ne ya wanke Jibril.

Lauyan masu shigar da kara, Ishaq Magaji ya bayyana ma kotun daukaka kara cewa wanda ake tuhuma ya tabbatar da cewa shi ya kashe mahaifinsa sa’annan ya binneshi cikin wata kabari, bayan musu daya barke tsakaninsu akan kudin dawa N56,000.

Daga karshe Lauya Ishaq Magaji ya bayyana jin dadinsu da wannan hukunci da kotun ta yanke, inda yace gaskiya ne kawai ta yi halinta, kuma yana fatan Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here