MAJALISAR KANO TA DAKATAR DA BINCIKEN GANDUJE

0
486
Gwamna Abdullahi Ganduje

Daga Usman Nasidi

MAJALISAR dokokin jihar Kano ta dakatar da binciken da take yi wa gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ne saboda yin biyayya ga umarnin kotu.

A ranar biyar ga watan Nuwamba ne wata babbar kotun jihar ta dakatar da majalisar dokokin daga binciken da take yi wa gwamnan sakamakon karar da wata kungiyar lauyoyi ta shigar inda ta kalubalanci majalisar.

Shugaban kungiyar Barrister Zubairu Muhammad ya yi zargin cewa majalisar dokokin jihar Kano ba ta da hurumin gudanar da bincike a kan Gwamna Ganduje kasancewar yana da rigar-kariya.

Sai dai a wancan lokacin, shugaban kwamitin Alhaji Bappa Babba Dan Agundi ya shaida abin da suka fuskantada hukuncin kotun shi ne \”mu ci gaba da bincke.\”

Ya kara da cewa za su je kotun ranar 12 ga watan Nuwamba don jin fassarar abin da take nufi.

Sai dai a zamanta na ranar 12 ga watan Nuwamba, kwamitin ya shaida wa kotun, wadda mai shara`a Ahmad Tijjan Badamasi ke jagoranta, cewa tuni ya dakatar da binciken har sai an kammala sauraren karar da kungiyar lauyoyin ta shigar.

Lauyan kwamitin, Barrister Mohammed Waziri, ya shaida wa manema labarai cewa tun da farko ma jahiltar umurnin da kotu ta bayar ne ya sa kwamitin tunanin ci gaba da binciken da yake yi.

\”Mun tabbatarwa kotu cewa majalisa ba za ta dauki wani mataki ba sai an gama wannan shari\’ar da ake yi. An ce mu dawo ranar 21 ga watan nan don haka an kusa gama shari\’ar ma.\”

Wasu masana shari\’a na ganin an kitsa kai batun zargin cin hancin da ake yi a gwamnan jihar ta Kano kotu ne domin a shiriritar da shi.

Sai dai wasu na ganin katu na da \’yancin sanya baki a kowanne sha\’ani da ya shfi gwamnati.

A watan jiya ne jaridar Daily Nigerian da ake wallafawa a shafin intanet ta fitar da jerin bidiyon da ya nuna Gwamna Ganduje yana cika aljihunansa da bandir-bandir na dalolin Amurka ta yi zargin cin hanci ne daga wurin \’yan kwangila.

Lamarin dai ya janyo ce-ce-ku-ce har ta kai ga majalisar lafa kwamitin da zai gudanar da bincike.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here