Kamfanin NNPC Ta Sallami Manyan Ma’aikata 80 Bayan Sun Fadi Jarrabawar Karin Girma  

0
497

Daga Usman Nasidi

KAMFANIN man fetur na Najeriya (NNPC) ta sallami manyan ma’aikatanta da suka kai matakin manaja su 80.

Kamfanin ta fara bayar da wasikun sallaman ga wadanda abun ya shafa a ranar Juma’a. A sashin Kaduna Refining and Petrochemical Company (KRPC), sama da ma’aikata 20 abun ya shafa.

Kakakin kamfanin Mista Ndu Ughamadu ya bayyana cewa an bukaci jami’an da abun ya shafa da su bar aiki saboda sun fadi jarrabawar karin girma wanda aka shirya masu kwanan nan.

\”Akwai wani jarrabawa na Karin girma sannan kuma wadanda basu yi kokari ba, ban san adadinsu ba yanzu, an nemi su ajiye aiki,” inji Ughamadu.

Akan dalilin da yasa aka sallami ma’aikatan maimakon hana su Karin girman, Ughamadu yace: “tsarin kamfanin haka yake sannan kuma hukunci hukumar ita ce hukunci.

Tsari ne da aka gudanar kuma wadanda masu yi kokari ba aka nemi su tafi. Hukumar kamfanin sun hadu akan haka sannan suka yanke hukunci cewa su tafi.” Ya bayyana cewa duk wani hakki na wadanda abun ya shafa za’a biya su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here