Matashi Ya Rasa Ransa A Hanun Masu Adawa Da Hana Mummunan Aski

0
625

Isah Ahmed Daga Jos

WANI matashi mai suna Aliyu Badamasi da ke zaune a garin Ramin kura, a Karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna, ya rasa ransa a hanun wasu matasa da suke adawa da ayyukan wata Kungiya da ke yaki da rashin tarbiyar da matasa suke yi. Na mummunan aski da sanya mummunan sutura da shaye shaye a garin, a daren ranar Talatar da ta gabata.

Shi dai wannan matashi  ya rasa ransa ne a lokacin ya fito daga gidansu don kiran yayansa, mai suna Abdurrahaman Badamasi wanda dan wannan Kungiya ne, lokacin da wadannan matasa masu adawa da hana mummunan aski suka zo suka far masa da duka. Shi ne daya  daga cikin matasan mai suna Maharazu Habu ya cakawa marigayi Aliyu Badamasi  wani makami a makoshi,  da ya yi sanadin rasa ransa.

Da yake yiwa wakilinmu karin bayani kan yadda  al’amari ya faru, wani kawun marigayin da aka yi abin kan idonsa, mai suna Malam Imirana Mu’azu Ramin Kura, ya bayyana cewa  ainihin abin da ya faru shi ne akwai wata Kungiya da aka kafa a garin. Ta koyawa matasa tarbiyar tare da yaki da mummunan aski da sanya mummunan sutura da shaye shaye da matasa suke yi.

Ya ce sai wadansu yaran wannan gari guda 22, da suke aikata irin wadannan miyagun dabi’u suka yi zanga zanga, kan nuna rashin amince da Kungiyar.

Ya ce shi ne aka  kama mutum 11 daga cikin wadannan matasa, aka yiwa kowannesu hukumcin  bulala 10 tare da yi masu aski.

Ya ce akwai wani mutum , da yake daurewa yaransa gindi, a wannan gari wanda  akwai  yaronsa mai suna Naziru Habu da yake cikin wadannan yara da suka yi zanga zanga.

Ya ce wannan mutum shi ne ya turo yaransa  zuwa gidan su marigayin don su bugi ‘yayan marigayin mai suna Abdurrahaman Badamasi wanda dan Kungiyar ne.

Malam Imirana ya yi bayanin cewa  marigayin yana tare da mahaifinsa mai suna  Badamasi Yakubu  a cikin gida,  sai mahaifin  ya ce ya tashi yaje waje ya ji hayaniya, kila yaran wannan mutumin ne  da ya ce zai turo su daki Abdurrahaman, ya ce  masa  ya dawo gida.

Ya  ce da marigayin  ya fito sai  ya sami wadannan yara ne da ake magana, suna ta dukan  yayan nasa Abdurhaman.  Sai marigayin ya shiga fadan.

‘’A cikin  wadannan  yara  akwai wani mai suna  Maharazu Habu sai ya fada gida a guje, ya dauko wani makami,  ya cakawa marigayin a makoshi.  Na kai masa kamu, sai na zame na fadi, ya yi cikin gida na bishi, ban sami kama shi ba, ya gudu. Daga nan muka dauki Aliyu muka tafi da shi asibiti,  inda ya rasu’’.

Ya ce marigayi Aliyu babu ruwansa da wannan magana,  mahaifinsu ne ya

aike shi ya kirawo yayansa  Abdurrahaman dan wannan Kungiya,  daga nan ajalinsa yazo a wajen, aka caka masa makamin  da ya yi sanadin rasuwarsa.

Ya ce a  rayuwarsa bai taba ganin irin wannan ta’adanci ba, don  haka duk lokacin da ya tuna wannan abu, sai hawaye sun zubo masa.

Shima a zantawarsa da da wakilinmu Sarkin  garin na Ramin kura, Alhaji Musa Idris ya bayyana cewa  gaskiya basu ji dadin faruwar wannan al’amari ba. Saboda ayyukan  alherin  da Qungiyar take yi a  garin.

Ya ce sune suka kafa Kungiyar domin ganin kowa ya zama mai tarbiya da ladabi, kuma kowa yarda da haka  a  garin.

Ya ce amma daga baya sai wannan mutum mai daurewa ‘yayansa gindi,  ya ce ‘yayansa ba zasu bi dokokin Kungiyar ba.

Sarkin ya yi bayanin cewa  Kungiyar zata cigaba  da ayyukanta, domin yara da dama sun sami tarbiya sakamakon  Kungiyar masamman wajen hana shaye shayen miyagun kwayoyi da askin banza da sanya sutura mara kyau.

Kakanki rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna DSP Yakubu Sabo ya tabbatar da faruwar wannan al’amari.  Ya ce ya zuwa yanzu wannan magana tanahanun Jami’an binciken aikata manyan laifuffuka na rundunar, kuma  da zarar sun  kammala bincike za a gurfanar da wadanda aka samu da laifi,

a gaban kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here