MUTANE 1,891 NE SUKA RASA RAYUKANSU A RIKICE RIKICEN FILATO

0
522

Isah Ahmed Daga  Jos

KWAMITIN mutum bakwai da Gwamnatin Jihar Filato ta kafa, don sake dawo da ‘yan gudun hijirar Jihar zuwa garuruwansu na asali. Ya bayyana cewa ya gano mutane 1,891 ne suka rasa rayukansu a rikice rikicen da aka yi, a Kananan Hukumomin Jos ta Arewa da Bassa da Riyom da Barikin Ladi da Bokkos da ke Jihar.

Shugaban Kwamitin Air Vice  Marshal Bala Danbaba ne ya bayyana haka,  lokacin da yake mikawa Gwamnan Jihar Simon Lalong rahoton Kwamitin, a gidan Gwamnatin Jihar da ke garin Jos.

Kwamitin ya ce ya gano cewa mutane 50,212 ne suka yi gudun hijira, daga ainihin wuraren da suke zaune a cikin al’ummomi 118 da wuraren da al’ummar Fulani suke zaune guda 98 zuwa wasu wurare daban daban, sakamakon wadannan rikice rikice.

Har’ila yau Kwamitin ya yi bayanin cewa ziyarci sansanonin ‘yan gudun hijirar wadannan rikice rikice guda 27, tare da karbar  takardun bayanai guda 55 daga al’ummomi da sauran mutanen da wadannan rikice rikice suka shafa.

Haka kuma Kwamitin ya ce ya gano  a wadannan rikice rikice an lalata Kauyuka guda 78 tare da lalata gonaki da kayayyakin amfanin gona a wadannan wurare da rikici rikice rikicen suka shafa.

Kwamitin ya kawo shawarar cewa gwamnati  ta dawo da mutanen da suka yi gudun hijirar  a duk lokacin ta fahimci cewa harkokin tsaro ya kyautatu a wadannan wurare.

Hakazalika Kwamitin ya shawarci gwamnati ta tanadarwa ‘yan gudun hijirar da suke son komawa garuruwansu na asali, kayayyakin da zasu sake gina gidajensu da aka lalata a lokacin rikice rikicen.

Da yake jawabi  lokacin da yake qavar rahoton, gwamnan Jihar ta Filato Simon Lalong ya bada tabbacin cewa gwamnatin Jihar zata yi nazarin rahoton Kwamiti tare da aiwatar da shawarwarin  Kwamitin batare da bata lokaci ba.

Ya yi kira ga al’ummar Jihar su cigaba da zaman lafiya kuma su guji yada jita-jita.

Shi da wannan Kwamiti,  gwamnatin Jihar ta Filato ce ta kafa shi,  tun a watan Yulin da ya gabata

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here