Sakamakon Shigowar Sanyi Cinikin Gwanjo Ya Kankama A Jos

  0
  722

  Isah Ahmed Daga Jos

  A DUK lokacin da yanayin sanyi ya shigo a kan ga mutane suna ta kokarin sayen kayayyakin sawa na gwanjo, kamar Jaket da Suwaita da Kwat da Safa da dai sauransu, domin yin kariya ga wannan yanayi.

  Har’ila yau a duk lokacin da wannan yanayi  ya shigo mutane suna rage yawan shan ruwa da sauran kayayyakin da suke da sanyi, domin samun saukin wannan yanayi.

  Ganin shigowar wannan yanayi na sanyi da aka shigo,  wakilinmu ya zagaya kasuwannin sayar da kayayyakin sawa na gwanjo da ke garin Jos da wuraren da ake sayar da ruwan sha da kayayyakin ‘yayan itatuwa, domin ganin yadda harkokin sayar da wadannan abubuwa suke tafiya.

  \"\"

  A lokacin da wakilin namu ya isa babbar kasuwar Jos, a bangaren ‘yan gwanjo ya ganewa idonsa yadda mutane suke ta sayen kayayyakin gwanjon.

  Hakazalika wakilin namu ya ziyarci babbar  kasuwar ‘yan gwanjo ta Katako da ke garin na Jos, nan ma ya tarar da kasuwar cike da mutane suna ta sayen kayayyakin gwanjon.

  \"\"

  Da yake zantawa da wakilinmu wani mai sayar da Gwanjo a Kasuwar mai suna Alhaji Ashura Babangida Isah  ya bayyana cewa kowa ya san yadda garin Jos yake da sanyi.

  Ya ce shi dai wannan kasuwanci na sayar da gwanjo yana yana tafiya a lokacin sanyi,  don haka  yanzu kasuwar gwanjo ta fara budewa a garin Jos.

  Ya ce yanzu mutane suna bukatar kayayyakin sawa na sanyi kamar Jaket da suwaita da kwat da Kadigan da safa. Don haka yanzu idan ka duba zaka ga masu sayar da gwanjo, kusan sun koma sayar da irin wadannan kayayyaki na sanyi.

  ‘’Kuma farashin gwanjon yana nan kamar yadda aka saba  bai tashi ba. Tun safe zaka ga mutane sun cika kasuwannin da ake sayar da gwanjo a wannan gari, musamman a babbar kasuwar gwanjo ta garin Jos’’.

  A lokacin da wakilinmu ya isa kasuwar ‘yan Lemo ta Katako da ke garin na Jos, ya zanta da tsohon shugaban Qungiyar masu sayar da ‘yayan itatuwa ta Najeriya Alhaji Salisu Abubakar Mai Lemo wanda ya bayyana cewa idan irin wannan lokaci  na sanyi yazo.  Lemo ya kan  bushe, amma Ayaba tana bukatar irin wannan yanayi.

  Ya ce amma maganar ciniki kuwa abu ne da Allah yake tafiyar da shi.

  Ya ce kayayyakin ‘yayan itatuwa kayayyaki ne da ake bukatarsu, domin kayayyaki ne na marmari da suke taimakawa rayuwar dan adam kamar Lemo da Ayaba, wadanda ko asibiti a kan ce  a baiwa marasa lafiya. Donhaka sanyi ko gumi baya hana cinikin ‘yayan itatuwa. Saboda haka  ko a lokacin sanyi suna samun ciniki gwargwadon hali.

  Shima a zantawarsa da wakilinmu wani mai masana’antar yin ruwan sha na Leda na Ray Smith da ke Unguwar Abadawa a garin Saminaka da ke Jihar Kaduna,  Mista Johnson Onwudiwe ya bayyana cewa  a wannan lokaci da sanya ya shigo kasuwar sayen ruwa ta kan ja baya.

  Ya ce amma  lokacin zafi kasuwar sayen ruwa tana tafiya sosai, amma idan lokacin sanyi ya shigo  cinikin ruwa ya  kan yi baya. Sai dai su yi hakuri su ajiye wasu motocin da suke kai ruwan zuwa wurare saboda rashin ciniki.

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here