Jihar Kwara: Wannan Takara Ne Tsakanin PDP Da Jami’an Tsaro – Gwamna Abdulfatah

  0
  455

  Daga Usman Nasidi

  GWAMNAN jihar Kwara, Alhaji Abdulfatah Ahmed, ya siffanta cika gurbin kujeran majalisan mazabar Ekiti, Isin, Irepodun da Oke-Ero a matsayin takata tsakanin jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP da jami’an tsaro.

  Gwamnan ya bayyana hakan ne cikin jawabin da mai magana da yawunsa, Muhyideen Akorede, ya saki yayinda yake nuna bacin ransa kan yadda aka gudanar da zaben jihar.

  Ya ce rahotannin da ya samu daga kananan hukumomi hudu da aka gudanar da zabe ya nuna cewa kama karya, cin zarafi, da cin mutuncin mambobin jam’iyyar PDP jami’an tsaro sukayi.

  Kana gwamna Ahmed ya yabawa mambobin jam’iyyar PDP da mabiyansu a mazabar da irin tsayawan da sukayi, da karfin halin da suka nuna duk da abinda jami’an tsaro sukayi.

  Mun kawo muku rahoton cewa jam\’iyyar APC ta lallasa PDP a zaben kujeran majalisan dokokin da aka gudanar a jihar Kwara jiya Asabar, 18 ga watan Nuwamba, 2018.

  Kanar Jamiyyar APC ta sanar da hukumar tsaro akan wanzuwar yan ta\’adda a wasu yankunan Jihar Kwara saboda zaben da aka shirya na ranar Asabar, 17 ga watan Nuwamba a Ekiti/Irepodun/Isin/Oke-ero.

  Mista Femi David, mataimakin Mr Raheem Olawuyi dan takarar APC, akan harkan watsa labarai ya jawo hankula akan hakan cikin wata sanarwa da aka bayar ga manema labaru ran Juma\’a a garin Omu Aran.

  Sanarwar ta bayyanar da cewa an shigo da yan ta\’addan ne da gangan domin tsoratar da masu kada kuri\’a a yayin zaben.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here