Mustapha Imrana Abdullahi
BAYANAN da ke fitowa daga Jihar Kano na cewa kimanin runfunan kasuwar Kurmi na Wuccin gadi ne suka Kone sakamakon gobarar da ta tashi a kasuwar da ke cikin birnin Kano a arewacin Nijeriya
Kamar yadda rahotanni suka tabbatar sun ce Saba\’in daga cikin wadannan rumfuna sun Kone kurmus, yayin da jami\’an Kashe Gobara suka samu nasarar Kashe wadansu bangarorin rumfuna Bakwai.
Ita dai wannan Kasuwa ta Kurmi ita ce tsohuwar Kasuwa a Kano da za a iya cewa ta haifi sauran kasuwannin da ke Kano, Amma duk da wannan tarihin da kasuwar keda shi rumfunanta na Wuccin gadi ne da akasarin su bugun kwano ne.