YADDA MAJALISA TA GWANGWAJE NAKASASSU A NAJERIYA

0
574

Rabo Haladu Daga. Kaduna

MAJALISAR dattawan Najeriya ta zartar da wata doka da ta yi gyara a kan matsalar nuna wariya ga masu larurar nakasa.

Majalisar ta dauki wannan matakin ne bayan ta karbi wani rahoto daga wani kwamiti, wanda ya yi nazarin kudurin dokar.

Shugaban kwamitin, Sanata Kabiru Marafa, ya shaida wa manema labarai cewa dokar ta kunshi abubuwan da suka shafi lamuran rayukan dan adam, kuma sai da suka nazarci bangarori da dama kafin bijiro da ita.

Ya ce akwai batutuwa da dama da aka duba da kuma wasu tanade-tanade da suka shafi \’yancin walwala da asibiti da gine-gine don ganin cewa masu irin wannan larura sun samu sauki a rayuwarsu.

Sanata Marafa ya ce wannan doka za ta kawo karshen duk wani kalubale da masu nakasa ke fuskanta kamar wariya a wurin samun aiki. Shin ya kamata masu nakasa su rika barace-barace?

Habibu Sani Babura: Malamin da bai san nakasa ba an tilasta wa mai nakasa yin fitsari a kwalba a jirgi \’Dokar ta sha ban-ban da sauran dokokin da ake fatali da su, domin wannan dokar ce da ta shafi wasu jinsi mutane da ke neman taimakon da kuma ke da \’yanci a dama da su a lamurar rayuwa,\’ inji Marafa.

Hakazalika a cewarsa, sai da suka tuntubi kasashe da dama kafin zartar da dokar, inda suka nemi shawarwarin hanyoyin tabbatuwar ta a cikin nasara.

Sanatan ya kuma kara da cewa babu aikin da zai gagari mai nakassa, abin da ake bukata kawai shi ne duba abin da ya dace da shi ba tare da ya zama kalubali ta kowanne fanin rayuwa ba.

Yanzu dai majalisar na dakon sa hannu bangaren zartarwa kafin dokar ta soma aiki a fadin Najeriya.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here