Boko Haram Sun Tare Sojojin Dake Kwashe Kayan Aiki Daga Metele, Sun Kwashi Makamai

0
532
  • Daga Usman Nasidi

A KOKARIN da Sojin kasar  Najeriya na su kwaso abokan aikinsu dake daji har suna rubewa yaci tura, bayan da suka sake arangama da mayakan Boko Haram dake kewayen dake wurin, kuma aka sake dauki ba dadi dasu, har ma sun sake karkashe su da ma kwasar makamai, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Alamu dai na nuna bayan wancan harin na Metele a Guzumala LGA, a makon jiya, mayakan Boko Haram ba tserewa suka yi ba, zamansu suka yi a yankin, kuma sun hana a shiga ko a fita daga garin.

Bataliya ta 119 ce dake Bagam inda sojojin suka hallara, taje domin ta kwaso gawarwakin na bataliya ta 157, amma sai aka sami asarar rayuka da manyan makamai.

Majiyarmu, tace, \”a safiyar jiya misalin 10:00am sun mana kwanton bauna, sun kuma sake kame mana mutane, sun kuma kwace motocin yaki na igwa da manyan bindigogi, amma munyi nasarar kwaso gawarwaki shuda daga wadanda muka je debowa\”

A shekaru kusan goma da ake wannan yaki dai, an sha korar Boko Haram daji, amma sai su dawo.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here