BUHARI YA YI MA YAN FANSHO KARIN KUDI DA KASHI 33

0
667

Daga Usman Nasidi

DAGA ranar Litinin na makon dake kamawa ne gwamnatin Najeriya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari zata fara biyan tsofaffin ma’ikata kudadensu na fansho na watanni shida har ma da karin kashi Talatin da uku da Buhari ya amince ayi.

sakataren kungiyar yan fansho ta kasa, Actor Zal ne ya bayyana haka a ranar Laraba 28 ga watan Nuwamba, inda yace sun samu wannan tabbacine bayan tattaunawarsu da shugaban hukumar fansho, PITAD, Sharon Ikeazor.

“Sharon ta bamu tabbacin duk tsofaffin ma’aikata zasu fara samun kudaden fanshonsu na watanni shida daga ranar Litinin, kuma mun gamsu da duk jawaban da ta yi mana a yayin wannan tattaunawa da muka yi da ita a babban birnin tarayya Abuja.” Inji shi.

A ranar 23 ga watan Oktoba ne kungiyan yan fanshon ta gindaya ma gwamnatin sharadin karin kudin fansho, inda suka bata kwanaki 21 lallai sai ta yi musu karin kudin fansho saboda samun karin albashi da ake sa ran zai fara aiki nan gaba.

Rashin cika musu wannan bukata zai tunzura yayan kungiyar yan fansho su gudanar da zanga zanga tare da mamaye hukumar PITAD da duk sauran ofisoshin da suka danganci biyan hakkokin yan fansho gaba daya, har sai an biyasu.

Sai dai shugaban PITAD, Sharon ta tabbatar musu da cewar a shirye suke su biyasu karin kamar yadda aka tsara, inda tace daga ranar Litinin mai zuwa yan fanshon da hukumarta ke kulawa dasu zasu fara karban kudadensu.

“Jimillan kudin da zamu biya na watanni shida shine naira biliyan shida da miliyan dari shida, N6.6bn, PITAD zata biya cikon sauran watanni shida da zarar ta samu kudaden da take nema daga wajen gwamnati.” Inji ta.

A cewar yan fanshon, tunda dai har gwamnatin tarayya, na jihohi da na kananan hukumomi sun amince da karin karancin albashin ma’aikaci a kasar, don haka ya zama wajibi akansu su yi duba ga tsofaffin ma;aikatan masu karbar fansho.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here