Jami’an Kwastan Sun Lakadawa Yaron Mota Duka Kan Kin Bayar Da Cin Hanci

0
769

Isah  Ahmed Daga Jos

WASU Jami’an Hukumar Kwastan, sun lakadawa  wani yaron motar J5 da ta dauko kayan bulawus, daga garin Onaca da ke kudancin kasar nan, zuwa garin Jos babban birnin Jihar Filato mai suna Aliyu Ahmed duka, a dajin Forest da ke kan hanyar zuwa garin Jos, a karshen makon da ya gabata.

Da yake zantawa da wakilinmu kan yadda al’amari ya faru, yaron motar  Aliyu Ahmed ya bayyana cewa suna ta howa daga Onaca zuwa Jos da misalin karfe 5 na asubahin wayewar garin ranar Laraba, suna tafiya.  Sai suka ga ana bin su a baya, ana cewa masu su tsaya.

Ya ce sai ya ce da direban su ya tsaya, bayan da suka tsaya sai suka ga ashe Jami’an kwastan ne.

\"\"

‘’Suka ce mu bude bayan mota sai na bude bayan motar. Suka fito da kayayyakin da muka dauko suka ga kayayyakin bulawus ne. Suka ce mu basu takardar kayan, muka basu. Suka duba sai suka ce mu kulle bayan motar. Suka ce suna son su yi magana da mai kayan. Sai muka kira masu Shugaban Kungiyar masu sayar da bulawus na kasuwar New Market da ke Jos, wanda sune masu kayan, muka gaya masa’’.

Aliyu Ahmed ya yi bayanin cewa  sai shugaba kungiyar  ya ce  ba zai basu komai ba. Saboda manyan jami’an Hukumar ta Kwastan  sun hana a basu qudi.

Ya ce sai na ce masu idan suna zargin kayan ne su tafi da shi  ofishinsu, idan kuma zasu sallame mu ne, su taimaka su sallame mu saboda gari yana waye wa.

Ya ce daga wannan magana, sai wani daga cikin su ya ce kada su yarda su gaya masu maganar banza. Wani  cikinsu ya ce idan suka yi wasa zasu yi masu dukan tsiya.

‘’Sai ni da maigidana  muka ce maye muka yi da har zasu yi mana duka. Ban gama rufe baki ba, sai wani ya cire dorina ya buga mani a ka. Ya kara kawo mani duka na biyu, sai na rike dorinar.Na ce masa maye na yi maka kake duka na? . Muna cikin haka sai sauran jami’an kwastan din su hudu suka rufar mani, wani ya daga gingin bindiga ya buga mani a ka. Wani ya sake buga mani bindiga a ka. Daga nan na fadi  kasa   basu qyaleni ba, suka ci gaba da buga mani sanda a ka,  daga nan na tashi’’.

Ya ce bayan haka sai suka zo, suna bashi  hakuri. Suka kawo masa ruwa domin ya wanke jikinsa saboda jinin da yake zuba.  Ya ce sai ya ce shi ba zai wanke jikinsa  ba. Domin sun zalunce shi. Ya ce daga nan sai  suka yi ta bashi hakuri.

Shima da yake zantawa da wakilinmu kan al’amari shugaban Kungiyar masu sayar da kayan bulawu na kasuwar New Market da ke garin Jos Alhaji Abubakar Isah Muhammad ya bayyana cewa daya daga daga cikin direbobin da suka dauko masu kaya daga Onacha zuwa Jos ne.  Yana  zuwa wannan  wuri sai jami’an kwastan suka tsare su. Suka tambaye su maye suka dauko?

 Ya ce sai suka gaya masu cewa sun dauko kayan bulawus ne,  suka kawo takardar da kungiyarmu da hukumar Kwastan suka yarda cewa kayanmu  da  muke sayowa  daga Onaca  da Legas babu wani karya doka,   suka nuna masu.

Shugaban kungiyar  ya yi bayanin cewa sai jami’an kwastan din  suka ce su basu kudi, sai suka ce  masu su abin da aka gaya masu ba zasu bada komai ba, sai dai su kira masu ni.

‘’Suka dauki waya suka kira ni suka tambaye ni kayan bulawus din  buhu nawa ne? na tabbatar  masu cewa buhu 15 ne. Kuma kayan bulawus ne da muka sayo daga Onaca. Sai  suka ce na basu officer on duty, wato wasu kudi da suke karva naira dubu 10 zuwa 15. sai nace masu ai wannan Hukuma   karqashin jagorancin Hamidu Ali ta gaya mana bata aiko mutanensu, su tare kayan da ba sune doka tasa a tare ba. Na ce  wannan gwamnati mai adalci, ta ce kada mu yi haka’’.

Ya ce sai suka koma wurin direban  suka ce ya basu wani abu. Sai ya ce masu su suna magana ne da yawun masu kaya. Kuma masu kaya sun ce kada su basu ko kwabo.

Ya ce daga sai  yaron motar ya ce ai tun da masu  wannan kaya, sun ce  ba kayan laifi bane sai ayi hakuri. Kawai sai suka hau shi da duka.

Ya yi kira ga Hukumar kwastan ta kasa  tayi bincike kan wannan al’amari, domin a hukumta wadanda suke da hanu a kai. Domin wannan gwamnati tana yaki da cin hanci da rashawa ne.

Amma a zantawarsa da wakilinmu kan al’amari babban jami’in hulxa da jama’a na Hukumar ta kwastan ta kasa DC Josheph Attah ya bayyana cewa abin  da jami’ansu da suke aiki a wannan waje suka ce   sun tsare  direban motar ne, amma yaki tsayawa  ya taho da gudu ya wuce.

Ya ce sun shiga mota zasu bi shi, sai suka ga  ya kauce daga hanya yaje ya fadi, sakamakon haka yaron motar ya sami raunuka a jikinsa.

Ya ce direban bai tsaya ba belle har jami’an su nemi ya basu wani abu, ya wuce da gudu ne ya je ya fadi.

Ya shawarci  ‘yan kasuwa  da direbobin da suke dauko masu  kayayyaki, su rika bin doka da oda.

Ya ce  wani lokaci halayen  da direbobin da suke daukowa ‘yan kasuwa kayayyaki  ne suke jawowa ‘yan kasuwar asara.

Ya ce idan direba yana tuka mota, idan yazo wajen da jami’an tsaro   suke bincike, idan aka tsayar da shi, ya kamata ya tsaya ya yi bayani.

‘’Idan mutum ya  dauki kaya na gaskiya duk jami’in kwastan din da ya ce dole sai ya    bashi cin hanci  ya ki.  Ya rike shedun ya kawo gabanmu,  mu kuma idan muka tabbatar, zamu hukumta shi  ta yadda  gobe ba kara ba’’.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here