Kungiyar Direbobin Tanka Zata Taimaka Wajen Wadata Kasar Nan Da Man Fetur-Tijani Zubairu

0
519

  Isah Ahmed Daga Jos

UBAN  Kungiyar Direbobin Tanka ta kasa [PTD]  Alhaji Tijani Zubairu ya bayyana cewa kungiyar zata  taimakawa kamfanin mai na kasa [NNPC], wajen ganin an wadata kasar nan da man fetur a lokacin bukukuwan sabuwar shekara mai zuwa, da  lokacin da za a gudanar da zabubbukan kasar nan, na shekara ta 2019.

Alhaji Tijani Yusuf ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi, a wajen taron kungiyar na wata uku da kaddamar da shugabannin kungiyar na shiyar Jos, da aka gudanar a karshen makon da ya gabata.  

Ya ce sun shirya wannan taro ne domin su tattatauna hanyoyin da zasu ga an wadatar da man fetur a bukuwan sabubawr shekara mai zuwa da  lokacin zabubbuka mai zuwa. 

Ya ce zasu tabbatar  an samar da wadatatcen man fetur a kasar nan. Don haka sun umarci dukkan shugabannin  kungiyar na dukkan shiyoyin kasar nan, su tabbatar an samar da wadatattacen mai a ko’ina a cikin kasar nan.

‘’Kamfanin mai na kasa ya tabbatar da cewa a shirye yake wajen baiwa ‘yan wannan kungiya goyan baya, ta hanyar samar da wadatattacen mai a qasar nan. Domin sun ce suna da mai da zai wadatar da kasar nan. Don haka muna kira ga dukkan ‘yan wannan kungiya  su baiwa kamfanin mai na qasa [NNPC] goyan baya da hadin kai, don  samar da wadatatcen mai a kasar nan. Kuma muna  umartar ‘yan wannan kungiya su cigaba da aiki har ranakun karshen mako, don ganin ba a sami matsalar karancin mai a Najeriya ba’’.

A  jawabinsa  Mataimakin shugaban kungiyar na kasa na biyu kuma kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautu na Jihar Filato Alhaji Dayyabu Yusuf Garga ya yi kira ga al’ummar kasar nan, su zauna lafiya musamman a wannan lokaci da zabubbukan shekara ta 2019  suka gabato.

Har’ila yau ya yi kira ga  shugabannin kungiyar na shiyar Jos da aka sake zaba, su cigaba da tafiya da kowa da kowa a  kungiyar.

Shima a nasa jawabin shugaban Kungiyar na shiyar ta Jos da aka sake zaba, Alhaji Danlami Muhammad ya bada tabbacin cewa yanzu suna da tankokin mai  sama da guda 80 dauke da man fetur a Deport na Jos. Don haka ya ce  ba za a sami matsalar karancin mai ba a wannan shiya, a lokacin bukukuwan sabuwar shekara.

Alhaji Danlami Muhammad ya yi bayanin cewa babban burinsa  shi ne ya ga  ya hada kan ‘yayan  kungiyar. Don haka ya yi kira ga ‘yayan kungiyar su cigaba da bashi goyan baya da hadin kai, domin ya cimma wannan buri nasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here