Muna Mutuwa, ku Biya Mu Hakkokin Mu Gwamnonin Arewa – Inji Ma’aikatan Jaridar NNN/GTK

0
576

Usman Nasidi Daga Kaduna

MA’AIKATAN kamfanin gidan Jaridar New Nigerian Newspapers da Gaskiya TaFi kwabo wadanda suka yi ritaya da wadanda ke kan bakin aiki sun yi kira ga masu kamfanin wato Gwamnonin Arewa dasu gaggauta kara kaimi wajen biyan ma’aikatan kamfanin duka hakkokin su domin yi musu adalci cikin sauki.

Ma’aikatan sun bayyana hakan ne a cikin wata takardar da suka rabawa manema labarai wanda yake dauke da sa hannun shugaban kungiyar Ma’aikatan Nicolas Dekera da sakataren ta Ibrahim Adamu, bayan wani zaman taron da suka yi a harabar kamfanin dake garin kaduna don neman mafita.

Kamfanin Jaridai dai ta dakatar da buga jaridu a takarda tun a shekarar 2015 inda suka koma buga labarai a yanar gizo a sakamakon barazanar matsalolin gudanar da harkokin kamfanin da suke fuskanta tun a wasu yan shekarun baya inda su kai ta gudanar yajin aikin har na tsawon wasu yan lokuta.

\"\"

Ma’aikatan sun kara da yin kira ga gwamnonin Arewa dasu gaggauta dawo da zancen sayar da kadarorin kamfanin wanda suka janye a sakamakon wani karar da aka shigar a kotu ada kamin a janye, domin a halin yanzu matsin rayuwar da mafi akasarin ma’aikatan suka tsinci kansu a ciki ya sanya wasu sun rasa rayukan su saboda basu da yadda za suyi su lura da kansu.

“Mafi akasarin ma’aikatan mu na cikin wani babban mawuyacin halin kuncin rayuwa saboda rashin biyan albashi wanda har ya haifar da korar wasu daga cikin gidajen da suke haya, wasu kuma basu iya biyan kudin makaranatun yaran su, bamu iya rayuwa tamkar kowa yadda ya dace don haka muke neman a biya mu hakkokinmu don muma mu yi rayuwa yadda kowa ke yi” inji su a takardar.

Ta kara da cewa “ a zahirin gaskiya, yanzu lokaci ya yi daya kamaci masu wannan gidan su duba halin da muke ciki domin yin duk wani abinda ya dace ta hanyar biyan duka wasu basusuka na albashi da muke bi da sauran hakkokin mu, kuma su bayyana mana matsayin mu a kamfanin sannan su yi duk yadda suke so ko abinda za su yi da wajen amma ba zaiyu mu ci gaba da zama a haka ba.”

Acewarsu, suna kyautata zaton wadannan gwamnonin za suyi musu adalci saboda ga dukkan alamu masu adalci ne tunda har suka fara kokarin sayar da wasu kadarorin kamfanin tun farko don biyan ma’aikatan hakkokin su, saboda haka suke kira gare su dasu ci gaba da wannan kyakkyawar manufar aikin da suka dauko.

Hakazalika, sun yabawa gwamnatin tarayya bisa ga kokarin da ta yi na fara biyan ma’aikatan kamfanin da suka yi aiki a karkashin ta kudaden su na fansho wanda ita ke hakkin biyan wadannan kudaden.

A karshe, takardan ta kuma bayyana mahimmancin namijin kokarin rawar da gwamnonin arewan suka taka wajen ganin cewa gwamnatin tarayyar ta gaggauta biyan ma’aikatan hakkokin su na fansho akalla 2.1 biliyan naira.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here