\’Yan Sandan Najeriya Na Cin Zarafin Wasu \’Ya\’yan Jam\’iyyar PDP A Sakkwato

  0
  561
  SUFETO janar na \'yan sandan Najeriya

  Rahoton Zubairu Sada

  JAM\’IYYAR PDP reshen Jihar Sakkwato ta yi tir da Allah wadai da halayen da hukumar \’yan sandan Najeriya take yi na musgunawa tare da cin zarafin wasu daga cikin \’yayanta ta hanyar kame tare da daure su babu gaira babu sabab, kuma ba tare da an gurfanar da su gaban kuliya ba domin su san irin nau\’in laifukan da suka aikata har hakan ta faru da su ba.

  Wannan bayani ya fito ne daga bakin Honorabul Abdullahi Yusuf Hausawa, sakataren yada labarai na jam\’iyyar PDP na Jihar Sakkwato a yayin da yake bayaninsa ga taron manema labarai wanda jam\’iyyar ta kira a ranar Lahadi 16 ga watan Disambar 2018.

  Honorabul Abdullahi Hausawa ya ce Allah ne shaida, kuma suna sanar da duniya cewa, sun gaji da rashin aminta da irin cin kashin da hukumar \’yan sandan Najeriya take yi wa  wasu \’ya\’yanta da magoya bayan PDP.

  Ya ce, \’yan sanda ya zuwa wannan lokaci sun rikide sun koma \’yan siyasa, suna nuna kiyayyarsu a fili da son ransu ko son zuciyarsu kadai saboda sun zama \’yan amshin shata ga jam\’iyya APC mai mulkin kasar nan.

  \’\’ Abin zubar da kima da mutunci wai \’yan sandan Najeriya suka yi tattaki tun daga Abuja zuwa Sakkwato da niyyar kamen wasu daga cikin \’ya\’yan PDP da ba su san hawa ba ba su san sauka ba aka ingiza keyarsu zuwa Abuja ba tare da an gaya masu laifukansu ba, kuma tamkar babu jami\’an \’yan sanda a Sakkwato. Kawai \’yan sandan Jihar Sakkwato sun ki amincewa da su aikata zalunci babu hujja.

  Hausawa ya ci gaba da cewa, abin bakin ciki shi ne \’yan sandan sun koma \’yan barandan sshugabancin APC na jihar a karkashin jagorancin tsohon Gwamnan Sakkwato, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko suna cin zarafin \’ya\’yan PDP. Ya ce, hakan ba za ta sabu ba, za mu bi duk wata hanyar da doka ta tanaza don bin kaddin mambobin namu na PDP da aka kama.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here