Jam\’iyyar PDP A Sakkwato Ta Koka Da Kiyayyar Da \’Yan Sandan Najeriya Suke Nuna Mata

  0
  558

  BAYANIN JAWABIN JAM’IYYAR PDP RESHEN JIHAR SAKKWATO GA MANEMA LABARAI DANGANE DA BATUN CIN ZAFI DA GARKAME WASU MAMBOBIN JAM’IYYAR DA HUKUMAR YAN SANDAN NAJERIYA SUKA YI

   

            Ya Ku Taron Manema Labarai,

            Babban dalilin wannan taro na manema labarai da jam’iyyar PDP reshen Jihar Sakkwato ta kira shine domin ta sanar da daukacin al’umma irin cin zarafin, wulakanci, cin fuska tare da kame da ba bias ka’ida ba da ake yiwa da yawa-yawan mambobin jam’iyyar tamu ba tare da an kai su zuwa kotu ba har a shafe mako daya ko makamancin haka.

            Yaku yan jarida, muna son duniya ta sani cewa, mun dawo daga rakiya da aminta da hukumar yan sandan Najeriya, wannan kuwa yana nuni ne da cewa, sun juye sun zama yan siyasa, suna zabar wanda zasu wulakanta domin son zuciyar su ne ya sanya suka zamanto yan amshin shata ga jam’iayyar APC suna aiwatar ko aikata yadda suke so a lokacin da suka ga dama.

            Ka duba abin mamaki ka gani cewa, wai Yan Sanda ne suka yiwo takanas ta Kano tun daga Abuja zuwa Sakkwato ba da niyyar komai ba sai ta yin kame da baya cikin ka’ida na Mambobin jam’iyyar PDP wadanda aka mayar da su Abuja kuma basu caje su da wani laifi ba suka yashe su a cikin ukuba da rashin jin dadi har fiye da mako guda.

            Hanyar sanya karfi da Yan Sanda suke yi domin su ji wa jam’iyyar adawa a Jihar Sakkwato itace kawai cin dunduniyar mambobinmu su cafke su ba gaira ba sabab, wannan al’amarin ya fara yin yawa a jihar, Yan Sandan sun zama makamin cin zarafi, cin mutunci da sanya tsoro a zukatan yan jihar tamu.

            Anfani da bangare na musamman na Yan Sanda masu fada da yan fashi da makami (SARS) domin suyi basaja domin cafko tare da tsare magoya bayan mu har na makonni biyu ba tare da an kai su kotu don a yanke hukunci ba, to hakan ma ya saba wa dokar kasa.

            Muna so mu tunasar da Sufeto Janar na Yan Sandan Nijeriya cewa, ba za mu kauce daga tsayuwarmu kyam ba na ganin an tabbatar da adalci ga dimbin magoya bayan jam’iyyarmu ba tare da wani jin tsoro ko shakka na dauri ba daga wadanda suke daukar nauyin kamfe na batanci ga jam’iyyarmu da cin mutuncin Gwamananmu da kuma al’ummar Jihar Sakkwato ba.

            Muna sane cewa, gungun Yan Sandan da aka turo Jihar Sakkwato su kama tare da tasa keyar wasu daga cikin magoya bayanmu wasu ne ga cikin wannan Yan Sanda na musamman wadanda Sufeto Janar na Yan Sanda ya kafa domin su rika kamo kowane mutum da yake adawa da Jam’iyyar APC ko gwamnatin tarayya.

            Zamuyi yi amfani da dukan abubuwan da Kundin Tsarin mulki ko Shari’a ta gindaya kan hakkokan mu ta fuskar Yancin cudanya ko na bayyana ra’ayin siyasa da na walwala. Babu wata irin ukuba da tsoratarwa da zata firgita mu wajen yin wannan aiki tukuru domin mu cimma tsare-tsaren zaben mu har ta kai dukan yan takarar mu a shekarar 2019 sun kai ga nasara Insha-Allahu.

            Muna fadin haka ne don mun ji balo-balo cewa, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi alkawarin babu sani-babu sabo da daidatawa tare da adalci tsakanin dukan Yan Nijeriya ba tare da jin tsoron ko alfarma ko sanayya daga kowa ba, wanda yayi hannun riga da ayyukan cin zarafi da rashin adalci da Yan Sanda suke aiwatarwa.

            Wani abin bakin cikida kwatance shi ne, a yayin da yan Usulin jihar mu da suka hada da magoya bayan jam’iyyarmu wasu da aka dauka dawainiyar su atsakiyar jihar suna tare su kulli yaumin suna yi masu fashi da makami, sai ga shi Yan Sandanmu sun rikide yan Siyasa, sun gaza tabuka komai wajen kamo yan ta’addan can su hana wannan muguwar barna, sun koma makamin cin fuska da cin zarafi ga al’ummar da suka taso da son zaman lafiya. Wannan biyayyar tasu a jam’iyyar ce muna iya cewa wasu daga cikin Yan Sandan a cikin Jihar suna da hadin gwiwa da mabarnatan nan suna jefa tsoro ga zukatan Yan Jihar Sakkwato masu son juna da zaman lafiya.

            Abin bakin ciki ne hukumar Yan Sandan Najeriya ta juye zuwa hukumar barna da jefa tsoro, kuma ta bari Shugabannin Jam’iyyar APC na amfani da ita ta hanyar tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Sanata mai ci a yanzu domin a ciwa dimbin magoya bayan mu mutunci. Wannan ihu bayan hari ne domin ya gaza cimma burin sa na ya batar da jama’ar Sakkwato cewa, shine wuka shi ne nama nasu. Yana da kishirwar sai ya tabbatar da ganin ana yamutsin Siyasa da sanya tsoro a jihar ta hanyar amfani da yake yi da ofishin Sufeto Janar na Yan Sanda.

            Yan Sanda anan Sakkwato basu bin son zuciyoyin su ba a lokuta da yawan gaske, A Yan kwanakin baya kadan ne rahoto ya zo cewa, Sufeto Janar na Yan Sandan Najeriya ya amince da bukatar APC ta Sakkwato domin chanzawa daya daga cikin Yaran tsohon Gwamna Aliyu Magatakarda Wamakko wurin aiki daga Kano zuwa Sakkwato inda zai Shugabanci hukumar Yan Sandan kwantar da tarzoma wato MOPOL 7 sake Sakkwato.

            Jami’in dan asalin Jihar Sakkwato ne, ya yi aiki a matsayin Babban Jami’in Tsaro (CSO) na Gwamna Wamakko a lokacin shekarun mulkin sa takwas. Ana zargin yana daga cikin Jami’an yan Sandan da suka jefa tsoro tare da kai hari da cafke magoya bayan Jam’iyyar adawa a wancan lokaci.

                                                                                                                                       Aiwatar da irin wannan ayyukan assha tare da yi wa doka karen-tsaye ba wani abin a-zo-a-gani bane ko abin daya taka-kara ya kare ba ne, domin a idanun tsohon Gwamna Wamakko na Jihar Sakkwato ma ana aikata su.

            Da wannan ne Jam’iyyar a matakin jiha tare da dimbin magoya baya masu biyayya ga dokoki ba za mu rungume hannuwan mu ba mu zura wa Yan Sanda idanu suna cin karen su babu babbaka suna kamewa tare da jefa Kazafi ga magoya bayan da basu ji ba basu gani ba, babu sididi babu sadada.

            Da haka ne muke cewa mun jera dukan wasikun da muka aike wa Yan Sanda da su na kararraki kan wadannan kai hare-hare ga ofis din Jam’iyyarmu da magoya bayan mu.

            A shirye muke mu bi duk wani matakin doka da muka ci karo dashi domin mu yaki tare da tabbatar da adalci ga dukan membobin mu don mu tsayar da zaman lafiya da zaman tare, da kuma ci gaban jihar da ma kasa baki daya.

  Sa Hannu

  HONORABUL ABDULLAHI YUSUF HAUSAWA

  Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP ta jahar Sokoto.

  1/12/2018

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here