Jam\’iyyar JMPP  Zata Kawo Sauyi A Najeriya- Alhaji Nazifi Dungurawa

  0
  551

  JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

  DAN takarar mataimakin gwamnan jihar kano a tutar jam\’iyyar  Justice Must Prevail Party, (JMPP) , Alhaji  Nazifi Ali Dungurawa yace jam\’iyyarsu zata kawo ingantaccen sauyi a kasarnan idan aka zabe ta a zabukan da za\’a gudanar a  shekara mai kamawa saboda kyawawan manufofin ta.

  Yayi wannan tsokaci ne a hirar  su da wakilin mu, inda ya kara da cewa JMPP itace kadai sabuwar jam\’iyya wadda take da  dan takarar shugabancin kasa da gwamnoni 36 da yan majalisun dokoki na kasa da na  jihohi kamar yadda tsarin dimokuradiyya ya tanadar, tareda yin kira ga yan Nijeriya dasu kara baiwa jam\’iyyar goyon baya domin ta cimma nasara a zaben da za\’ayi.

  Alhaji Nazifi Ali Dungurawa ya sanar da cewa lokaci yayi da za\’a zabi matasa cikin gwamnati saboda   yanzu zamani  ya canza salo kuma matasa ake son gani a sahun gaba wajen jagoranci bisa tsari iran na dimokuradiyya musamman yadda matasan suke da basirar mulki da kuma sanin ya kamata.

  Sannan ya nunar da cewa da yardar Allah, jam\’iyyar su ta JMPP zata  samar da ci gaba mai  ma\’ana a kasa da kuma jihar kano saboda kyawawan tanade-tanaden da take dasu na alheri ga al\’uma a birane da kuma  yankunan karkara  inda kuma ya bukaci al\’umar jihar kano dasu zabi Alhaji Ghali Auwalu Goro a matsayin gwamnan jihar a tutar jam\’iyyar JMPP  domin samar da sauyi mai albarka.

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here