AN SAKA DOKAR TAKAITA ZIRGA-ZIRGA A ZAMFARA

0
576

Daga Usman Nasidi

HUKUMAR \’yan sandan Najeriya reshen jihar Zamfara ta bayar a sanarwar takaita zirga-zirga a karamara hukumar Tsafe da ke jihar sakamakon zanga-zangar nuna damuwa kan yawaitar kashe-kashe a jihar wadda daga bisani ya haifar da rudani da kone-kone.

Rahotanni sun bayyana cewar wasu matasa sun fito suna zanga-zangar nuna damuwar su kan lamarin rashin tsaro a jihar inda aka ce sun rufe tittin da ya sada Funtua, Zaria, Sokoto, Kebbi da Kaduna.

Rahotanni sun ce matasan sun kona sakatariyar karamar hukumar na Tsafe kuma sun nufi gidan shugaban karamar hukumar.

Jami\’n hulda da jama\’a na \’yan sandan jihar, Mohammad Shehu ya sanar da cewar an al\’umma za su iya fitowa suyi harkokinsu ne daga karfe 7 na safe zuwa karfe 6 na yamma kamar yadda Cable ta ruwaito.

Ya ce dokar takaita zirga-zirgar za ta cigaba da aiki har sai nan gaba idan abubuwan sun lafa a garin.

\’Yan ta\’adda sun kai hari a kauyen Magami da ke karamar hukumar Maradun a ranar Asabar inda suka kashe mutane da dama.

Tuni dai hukumar \’yan sandan ta bayar da umurnin aikewa da karin \’yan sanda zuwa jihar na Zamfara domin su taimaka wajen bin sahun \’yan ta\’addan tare da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al\’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here