Sojoji 13, Dan Sanda 1 Sun Mutu Yayin Sabon Artabu Da \’Yan Boko Haram

0
491

Daga Usman Nasidi

RUNDUNAR sojojin Najeriya ta ayyana cewa jami\’an ta akalla 13 ne da kuma wani jami\’in \’yan sanda suka rasa rayukan su yayin wani kwanton bauna da mayakan Boko Haram suka kai masu a sansanin su dake daya daga cikin garuruwan jihar Borno.

Mataimakin babban Daraktan hulda da jama\’a na rundunar Operation Lafiya Dole, Kanal Onyema Nwachukwu shine ya tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Talata.

Kanal Onyema Nwachukwu ya kara da cewa mummunan lamarin ya auku ne lokacin da rundunar ta tura jami\’an ta sintiri a kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.

Ya kara da cewa dakarun nasu sun yi iya bakin kokarin su suga cewa sun samu galaba akan \’yan ta\’addan amma Allah bai nufa ba har dai suka rasa ran na su.

Amma sai dai Kanal Onyema Nwachukwu ya bayar da tabbacin cewa za su kara kaimi wajen ganin sun kakkabe dukkan sauran \’ya ta\’addan daga maboyar su a ko ina ne.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here