Uba Ya Ba Yarsa Me Shekara 3 Guba Saboda Ta Fiye Kuka A Kano

0
473

Daga Usman Nasidi

WANI mazaunin karamar hukumar Rimin Gado da ke jihar Kano, Sani Kofar-Gabas ya kashe yar’sa mai shekara uku da maganin kashe kwari.

Da yake tabbatar da lamarin, Magaji Majiya, kakakin yan sandan jihar, ya fada ma manema labarai a raar Litinin cewa Misata Kofar-Gabas ya ba yar’sa maganin kwari wato piya-piya biyo bayan wani karyewa da tayi a kafa.

A cewa Majiya, mai laifin wanda ya amsa laifinsa, yace ya fusata da yar nasa saboda ta fiye kuka ba gaira ba dalili saboda raunin da ta ji a kafar ta.

Ya kara da cewa marigayiyar ta fara amai bayan ta sha gubar sannan Kofar-Gabas ya nuna kamar bai san abunda yarinyar ta sha take amai ba sannan ya dauke ta zuwa asibiti inda aka tabbatar da mutuwarta.

Kakakin yan sandan yace bad a jimawa ba za a gurfanar da mai laifin a gaban kotu domin fara shari’a.

Da yake Magana a madadin ahlin gidan, kakan marigayiyar na wajen uwa yace za su tabbatar da cewar an hukunta Saminu Sule akan kashe yar’sa da yayi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here