YAN BINDIGA SUN KASHE JAGORAN APC DA WASU 19 A ZAMFARA

0
527

Daga Usman Nasidi

‘YAN ta’adda sun dawo da kai hare-hare a garuruwan jihar Zamfara, inda suka kashe mutane 20 ciki har da jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na jihar, Alhaji Aliyu Abbas, jaridar Leadership Hausa ta ruwaito.

‘Yan ta’addan sun kai hari garin Magami dake karamar hukumar Maradun inda suka budewa marigayin wuta ya kuma mutu a nan take, wani da aka yi abin a gabansa ya bayyana cewa, bayan da suka kashe Abbas ne suka kuma bude wuta a kan jama’a in da mutane 19 suka rasa ransu.

Sarkin Maradun, Alhaji Garba Tambari ya bayyana wa mukaddashin gwamnan da sauran manyan jami’a rundunonin tsaron jihar cewa, jami’an tsaron da ke yakar ‘yan ta’addan na dari-dari da ayyukansu, ba sa aikin da yadda ya kamata.

Ya yi mamakin yadda jami’an tsaron ke gudun yin gaba da gaba da ‘yan ta’addan a duk lokacin da suka kawo hari.

Ya kuma kara da cewa, lokaci ya yi da jami’an tsaro za su yi azamar ganin kawo karshen ‘yan ta’addan a jihar zamfara gaba daya.

Sarkin ya kuma bayyana cewa, a haka yanzu garuruwa da kauyuka da daman a karkashin mulkin ‘yan ta’adda.

Shugaban karamar hukumar, Honarabul Yahya Shehu ya nuna damuwarsa a kan ayyukan da jamoi’an tsaron ke yi a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here