Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Raba Wa Sarakuna Masu Daraja Ta Daya Motocin Alfarma 

0
680

Mustapha Imrana Daga Kaduna

GWAMNATIN Jihar Kaduna ta raba wa motocin alfarma ga sarakuna masu daraja ta daya a jihar. An raba motocin alfarma kirar Peugeot 508 guda 10 ga sarakuna masu daraja ta daya da kuma mota kirar Lankuruza Jip (Landcruiser Jeep) guda daya ta Shagaban Majalisar Sarakunan jihar a yau Litinin 24 Dizamba, 2018 a nan Gidan Gwamnati da ke Sa Kashim Ibrahim.

Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kaduna, Hon. Bashir Sa’idu  ya mika kyautan wadannan motocin a madadin GwamnanJihar Kaduna.

Shugaban Ma’aikatan , a yayin da yake mika wadannan motoci ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Kaduna ta dauki wannan mataki ne na raba wa sarakuna motoci a kokarin da gwamnatin ta ke yi na dawo da martabar sarauta a jihar musamman lura da irin gudummuwar da sarakunan ke bayarwa wurin tabbatuwar zaman lafiya a jihar.

In ba a manta ba, watannin baya ma, Gwamnatin Jihar Kaduna ta raba wasu jerin motoci ga sarakuna masu daraja ta biyu da ta uku a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here