Karamar Hukumar Lere Zata Kashe Naira Biliyan 2.9 A Shekara Ta 2019

0
526

 Isah Ahmed Daga  Jos

Karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna zata kashe kudi N2,977,036,146 a kasafin kudin ta na sabuwar shekara ta 2019. Shugaban Karamar Hukumar Alhaji Abubakar Buba ne ya bayyana haka, lokacin da yake yiwa wakilan al’ummomin Karamar Hukumar bayanin kan kasafin kudin, a garin Saminaka. 

Ya ce a  kasafin kudi karamar hukumar tana sa ran samun N2,274,923,732 daga kason gwamnatin tarayya, da N82,527,400 daga gwamnatin Jiha da N565,537,154 daga harajin VAT da kuma N44,047,860 daga kudaden shiga na haraji da za a tara a karamar hukumar.

Ya ce za a kashe N1,510,737,420   na kasafin kudin  wajen biyan ma’aikata albashi da sauran harkokin gwamnati.

Har’ila yau ya ce za a kashe N1,466,298,726  na kasafin kudin wajen gudanar da ayyukan raya kasa a karamar hukumar.

Ya ce a shirya  kasafin kuxi ne bisa ga abubuwan da al’ummar karamar hukumar suke bukata domin sai da aka  yi zama da dukkan wakilan su  aka tuntube su, kafin  ayi kasafin kudin.

Abubakar Buba ya yi bayanin cewa   karamar hukumar ta kafa wani  kwamiti da  zasu bi yadda za a kashe kudaden da aka yi a kasafin kudin, don ganin ana kashe kudaden kamar yadda aka tsara.

Ya ce wannan kwamiti akwai ‘yan bangaren gwamnati da ke karkashin shugabancin  Shu’aibu Sulaiman  da ‘yan bangaren kungiyoyin sa kai, da ke karkashin shugabancin Madam Ladi Bonet.

Ya ce aikin wannan kwamitin ne ya duba abubuwan da aka yi, sun daidai ko basu daidai ba, ya  bayar da rahoto.

Ya ce lokaci ya wuce da gwamnati zata zauna ta kashe kudaden  al’umma batare da tayi masu bayani ba. Don haka   ya ce duk bayan wata uku zasu rika tara al’ummar karamar hukuma, su gaya masu abubuwan da suka yi da kudaden karamar hukumar da aka basu.

‘’Babu shakka daga lokacin da muka zo zuwa yanzu mun sami nasarori da dama kan ilmi da kiwon lafiya da samar da ruwan sha da hanyoyin mota da  samarwa matasa ayyukan yi.’’

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here