BOKO HARAM SUN KWACE GARURUWA 6 A BORNO

0
616
\"\"

Daga Usman Nasidi 

RAHOTANNI da ke zuwa mana sun yi ikirarin cewa yan ta’addan Boko Haram sun kwace garuruwan Baga, Doron-Baga, Kross Kawwa, Bunduran, Kekeno da kuma Kukawa a jihar Borno.

Wata babbar majiya ta sojoji da siyasa ne suka bayyana hakan a Maiduguri a ranar Lahadi, 30 ga watan Disamba.

An tattaro cewa dukkanin garuruwan guda shida sun kasance manyan cibiyoyi a karamar hukumar Kukawa da ke yankin arewacin Borno a yanzu haka babu dan Najeriya ko wata runduna a yankunan.

Yan ta’addan sun fara kai hari wani sansani na rundunar tsaro da ke Mil Hudu (wani yanki a wajen garin Baga) da misalin karfe 4pm sannan sojoji suka mayar da martani.

Rahoton ya kuma yi ikirariun cewa ana ta arangama har tsakar dare inda daga bisanin yan ta’addan suka kwace sansanin ojin yayinda sojojinmu suka ja da baya.

An kawo cewa kwamandan rundunar, wanda aka bayar da sunansa a matsayin Birgediya Janar Hassan ya tsere cikin dare zuwa wani sansani na yan sanda da ke garin Baga tare da wasu jami’ansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here