Mutane Suna Barin Gidajensu Yayin Da Boko Haram Ke Mamaye Garuruwa A Borno

0
625

Daga Usman Nasidi 

MUTANE da dama suna barin gidajensu daga jihar Borno suna ficewa ta garin Damaturu zuwa garuruwan Bauchi, Kebbi, Zamfara da Jigawa yayin da Boko Haram ke mamaye wasu garuruwa a Borno.

Mazauna garuruwan sun shaidawa Punch cewa \’yan ta\’addan Boko Haram din da suka kai hari wasu garuruwan Borno suna kokarin kaiwa sojoji hari ne.

A makon da ta gabata, mayakan Boko Haram sun mamaye garuruwan Baga, Doron-Baga, Kross Kawwa, Bunduran, Kekeno da Kukawa bayan sun shafe kwanaki 3 suna fafatawa da dakarun soji.

Mallam Bukar Kachalla da Mr Abacha Musa sun shaidawa majiyar Legit.ng a wayar tarho cewa sun ranar Lahadi mutane suna ta ficewa daga jihar ta garin Dapchi da Damaturu zuwa jihohin da ke makwabtaka da Borno kamar Jigawa, Kebbi, Bauchi, Zamfara da Gombe.

\”Baga babban gari ne na masunta kuma mutane da dama musamman hausawa sukan zo garin domin sana\’ar kifi amma bayan harin mutane da dama sun bar garin,\” inji Abacha.

\”Daya daga cikin wanda suka bar garin, Mallam Isa Haruna ya ce mayakan Boko Haram da suka zo garin Baga suna da saukin kai har ma sunyi sallah tare da mutanen garin a masallaci guda daya.

\”Babu ruwansu da mu fararen hula, sojoji suke nema su kashe.\”

Abacha ya ce wadanda suke barin garin sun bayyana cewa suna shan wahala sosai saboda tafiyar kasa da su keyi kafin su samu motoccin hawa zuwa Damaturu.

A bangarensa, Abacha ya yi mamakin yadda Boko Haram suka tsananta hare-hare yanzu da zabe ya karato.

Ya yi kira ga kasashen duniya su taimaka wurin kawar da Boko Haram daga arewa maso gabas domin samun zaman lafiya da tsaro a yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here