\’Yan Bindiga Sun Kashe Fasinjoji 4, Sun Raunata Wasu 2 A Barikin Ladi

0
509

Daga Usman Nasidi 

WASU \’yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari a jihar Plateau inda suka kashe mutane hudu a garin Nding da ke karamar hukumar Barkin Ladi na jihar.

Jami\’in hulda da \’yan sanda na jihar, Terna Tyopev ya tabbatar da afkuwar harin yayin hira da ya yi da menema labarai a ranar Litinin a Jos kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Mista Tyopev ya ce wannan mummunan lamarin ya afku ne a yammacin ranar Lahadi yayin da wasu mazauna kauyen ke komowa garin a cikin wata mota kirar Peugeot 504 station wagon.

\”Jiya, misalin karfe 6:15 na yamma wani Mr Samson Bitrus na kauyen Nding ya kira mu inda ya ce wasu \’yan bindiga sun kai hari ga fasinjojin wata Peugeot 504 Wagon a hanyarsu na komawa gida.

\”Ba tare da bata lokaci ba kwamishinan yan sandan jihar, Austin Agbonlahor ya aike da tawagar \’yan sanda wurin da akayi fashin amma ko da suka isa wajen \’yan bindigan sun tsere.

\”Yan sandan sun tarar da mutane uku a kwance kuma suka garzaya da su zuwa asibitin Barkin Ladi cikin gaggawa inda likita ya tabbatar da cewa sun mutu.

\”Cikin mutane uku da suka jikkata, daya ya mutu a asibiti yayin da sauran biyun suna nan suna jinya,\” inji shi.

Mai magana da yawun \’yan sandan ya ce an fara gudanar da bincike domin gano wadanda suka aikata wannan mummunan aikin kuma ya yi kira ga al\’umma da suke da wani bayani mai amfani su sanar da \’yan sanda domin taimaka musu.

Daga karshe, ya shawarci mazauna jihar su cigaba da biyaya ga doka da oda wajen gudanar da harkokinsu na yau da kulum.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here