Sheikh Jingir Ya Nuna Juyayi Kan Garkuwa Da ‘Yan Agajin Izala Mutum 20

0
1019
Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir,,,,,

Isah Ahmed Daga Jos

SHUGABAN Majalisar Malamai na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya nuna juyayinsa kan yadda masu garkuwa da mutane suka yi garkuwa da ‘yan agajin kungiyar mutum 20, a karshen makon da ya gabata. Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya nuna juyayin nasa ne a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida, a garin Jos.

Ya ce babu shakka ya shiga damuwa kwarai da da gaske kan wannan abu da ya faru. Domin ‘yan agajin nan da dare da rana suna aikin taimakon jama’a  ne, batare da biyansu albashi ba. Wani ya rike su ya ce su bashi kudi,   wannan akwai daukar alhaki kuma akwai rashin tausayi.

Ya ce don haka yana  rokon masu Garkuwa da mutanen  su ji tsoran Allah su sako  wadannan  ‘yan agaji da suka yi Garkuwa da su.

‘’Abin da ya same ni shi ne a ranar lahadi 23 ga watan disambar da ya gabata,  an kama mani ‘yan agaji mutum 20, bayan sun dawo daga wajen taron atisaye da aka gudanar a Jigawa. Suna  kan hanyar dawowa zuwa Jihar su ta Sakkwato, sun shiga yankin  Jibiya da ke Jihar Katsina, zasu shiga  Jihar Zamfara sai suka hadu da  wadannan mutane  suka tsayar da su, suka fito da su daga mota, suka tafi da su cikin daji suka bar motar a wajen. Don haka ina cikin matsala kan kama wadannan ‘yan agaji, amma muna nan muna ta yin addu’a’’.

Sheikh Jingir ya  jajantawa iyalan  ‘yan agaji kan faruwar wannan al’amari, kuma ya yabawa kungiyoyin ‘yan agaji Fitiyanu da ‘Yan darikun Kadiriya da Tijaniya da sauran kungiyoyin addinin musulunci daban daban, kan yadda suke ta yi masa jaje kan wannan al’amari.

Daga nan ya yi kira ga gwamnatoci da malaman addini da sauran shugabannin al’umma  a taru a baiwa tsaro mahimmanci, domin tsaro na kowa da kowa ne.

Har’ila yau ya yi kira ga gwamnati ta samar da kayayyakin tsaro na zamani ta baiwa sojoji  da sauran jami’an tsaron qasar nan. Kuma  ta hada kai da kasashen da suke makotaka da Najeriya domin a magance matsalar tsaro da ake fama da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here