Yadda Aka Gudanar Da Taron Ranar Kabilar Duguza A Jos

0
646

Isah Ahmed Daga  Jos

AL’UMMAR Kabilar Duguza daga kowanne bangare na Najeriya, sun gudanar da babban taron tunawa da ranar kabilar, a garin Jos babban birnin Jihar Filato. 

A wajen taron an gabatar da jawabai da raye rayen gargajiya na Kabilar da kuma rantsar da sababbin shugabannin kungiyar kabilar na kasa.

Da yake jawabi a wajen taron wani dan kabilar kuma dan majalisar dokoki ta Jihar Filato, mai wakiltar mazabar Pengana da ke Karamar Hukumar Bassa Honarabun Ezekiel Bauda Afon ya bayyana cewa ada mutane basu san Kabilar Duguza ba, amma yanzu sun kai wani mataki da aka san su a duniya.

\"\"

Ya ce Kabilar Duguzawa suna nan a ko’ina a Najeriya,  don haka suna nan suna bincike domin  gano duk inda  suke a Najeriya.   

Mista Afon ya yi bayanin cewa harshen  Duguza yana da matukar mahimmanci, don haka ya yi kira ga kwamitin bunkasa harshen  Duguza da aka kafa, su yi kokari su inganta aikinsu don ganin an bunkasa harshen.

\"\"

A nasa jawabin babban Bako mai jawabi Mista Najuba Ayuba ya yi kira ga  iyayen kabilar  su taimakawa ‘yayan kabilar  ta hanyar daukar su aiki a wurare daban daban.

Ya yi  kira ga al’ummar  jihar Filato da Najeriya baki daya a zauna lafiya,  domin sai da zaman lafiya za a sami cigaba.  

Daga nan ya roki  Allah ya baiwa Najeriya  shugabanni masu  tausayi da zasu  kawo zaman lafiya  da cigaba a Najeriya.

A nasa jawabin Sarkin Magama Gumau da ke Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi Malam Musa Sambo Duguza,  ya bayyana cewa wannan babbar rana ce ga dukkan ‘yan kabilar Duguza. Domin a duk shekara suna taruwa a irin wannan rana, don  gudanar da irin wannan taron  sada zumunci da  tattauna abubuwan da zasu kawo masu cigaba.

Ya yi kira ga dukkan ‘yan kabilar  su rumgumi harkokin neman ilmi da  sana’o’i.

Tun da farko a nasa jawabin sabon shugaban kungiyar kabilar na kasa, Barista Sale Magama ya yi ga kira ga al’ummar Duguzawa su basu goyan baya da hadin kai, domin su kai ga nasara.

Ya  ce babban burinsu shi ne su hada kan al’ummar Duguzawa wuri daya, domin su aiwatar  da abubuwan da zasu kawo wa kabilar  cigaba.

Ya bada tabbatacin cewa zasu yi aiki ba  dare ba rana, domin ganin sun  yi abubuwan da suka yi kudurin yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here