Zan Hukunta Duk Wanda Aka Samu Da Hannu A Rikicin Kasuwar Magani – El-Rufai

0
606

Daga Usman Nasidi 

GWAMNAN jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya sha alwashin cewa gwamnatin sa ba za ta zuba idanu kawai tana kallon wadanda suka tada rikicin da ya auku a Kasuwar Magani ba.

El-Rufai ya ce duk wanda bincike ya bayyana yana da hannu a wannan rikici zai dandana kudan sa domin gwamnati za ta hukunta shi kamar yadda doka ya tanadar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a taron da yayi da mutanen garin Kasuwar Magani da kewaye inda ya shaida musu cewa lallai gwamnati za ta hukunta duk wanda ta samu da laifi a wannan rikici.

Idan ba a manta ba Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Kaduna, ya bayyana cewa an kashe mutane 55 a kazamin rikicin da aka yi a watan Oktoba, a garin Kasuwan Magani, cikin Karamar Hukumar Kajuru, a jihar Kaduna.

Kwamishina Ahmed Abdur-Rahman ya bayyana haka ne da yake zantawa da manema labarai a Kaduna,sanna kuma ya ce ‘yan sanda sun kama mutane 22 da ake zargi da hannu a wajen tayar da kayar bayan.

Hakimin Kufana, Titus Dauda ya bada shawarar a karo jami’an tsaro a wannan yanki cewa hakanne kawai zai kawo karshen irin wannan tashin hankali da ake fama dashi a wannan yanki.

Suko kungiyoyin addinai na Musulmai da Kirista shawarar su daya ne cewa idan ba hukunta wadanda suke tada irin wannan tashin-tashina ake yi ba ba za a taba samun zaman lafiya ba. Sun kara da cewa gwamnati ta rika hukunta masu tada irin wannan rikici cikin gaggawa shi ne mafita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here