Sojoji Da DSS Sun Mamaye Kamfanin Jaridar Daily Trust Gida Da Waje

0
557

Daga Mustapha Imrana Abdullahi Da Usman Nasidi

JAMI\’AN tsaron soja da jami\’an tsaro na cikin gida DSS a tarayyar Nijeriya sun kai wani samame a ofishin jaridar Daily trust da ke garin Maiduguri da kuma hedikwatarsu da ke babban birnin tarayya Abuja.

Bayanan da muke samu daga bakin ma\’aikatan jaridar ta daily trust bayan sun Kai Samame Ofishin Jaridar da ke babban birnin Jihar Barno a Mai duguri sun kuma Kai Samame babban Ofishin jaridar da ke Abuja inda bayan sun kammala bincikensu suka tilastawa ma\’aikatan da suke aiki a dakin tattara labarai suka kuma umarcesu da su fice daga ofishin kamar yadda ma\’aikatan suka tabbatar wa da wakilinmu.

Amma ya zuwa lokacin da aka rubuta wannan labarin babu wata hujja Ko dalilin yin hakan.

\"\"/

Sai dai cibiyar yan jaridu ta kasa reshen birnin tarayya Abuja ta fitar da wata sanarwa inda ta ke shaidawa daukacin manema labarai na Abuja da duniya baki daya cewa suna nan suna duban irin yadda lamarin ke faruwa don haka a kwantar da hankali.

Yayin da daukacin yan Jarida a Nijeriya da duniya baki daya ke kokarin sanin ko meye dalilin sojojin na yin wannan aika aika a ofisoshin jaridar daily trust

Rahotanni sun bayyana cewar sojojin da kuma wasu jami\’an tsaro sanye da farin kaya sun zagaye ofishin inda suka hana shige da fice.

Mataimakin babban editan jaridar Mahmud Jega ya fada ma BBC cewa sojojin sun isa ofishin da kimanin karfe 4 na yamma, kuma sun kutsa ciki da karfe 5.33.

\”Sojoji sun rufe ofishinmu na Maiduguri da safiyar ranar lahadi, kuma sun tafi da wasu ma\’aikatanmu biyu. A halin yanzu suna tsare da su a can\”.

Har yanzu babu wani bayani daga jami\’an sojoji ko na jami\’an DSS game da dalilinsu na kai wannan samamen.

Daga nan sojojin sun bukaci dukkan ma\’aikatan su taru a wuri guda kuma sun gudanar da bincike akan ma\’aikatan da ke cikin ofis.

Binciken ya bayyana cewar sojojin sun kai wa jaridar ta Daily Trust wannan samamen ne saboda babban labarin da ta wallafa a ranar Lahadi a shafinta na farko.

\”Sun bukaci dukkan ma\’aikatanmu su fice daga harabar ofishin, kuma sun kwace dukkan na\’urorin aiki a hannun ma\’aiakatan namu\”, inji Mahmud Jega.

Har lokacin da ake hada wannan rahoton sojojin na cikin harabar ginin kuma sun kashe wutar ginin baki daya.

Hakazalika a Jihar Kaduna, kungiyar ‘yan Jaridu rashen Jihar ta fitar da wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren kungiyar Kwamared John Femi Adi inda yake umartar yayan kungiyar da kowa ya kwantar da hankalinsa 

\”Kasancewar su ma\’aikatan bangaren jaridar daily trust masu aiki a bangaren labarai ba su a cikin NUJ, Amma tun da membobi ne na kungiyar ‘yan Jarida hakika abin da aka yi masu ya sabawa tsarin aikin kuma ana nan ana duban lamarin da idanun basira\”.

Duk da yake abin da daukacin manema labarai ke cewa shi ne menene dalilin da yasa sojoji suka dauki wannan matakin?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here