GWAMNATIN TARAYYA TA AMINCE DA SABBIN JAMI’O’I 4

0
738

Daga Usman Nasidi 

RAHOTANNI sun kawo cewa a zaman da bangaren zartarwa ta yi a ranar Laraba, 9 ga watan Janairu, gwamnatin Tarayyar kasar ta amince da kafa sabbin jami’o’i masu zaman kan su a kasar.

Ministan ilimi Adamu Adamu ne ya sanar da hakan ga manema labarai jim kadan bayan kammala zaman kwamitin zantarwa da ma’aikatar ta yi.

Ga jerin sunayen jami’o’i da aka amince da su mun kawo maku a kasa:

1. Jami’ar Greenfield a jihar Kaduna

2. Jami’ar Dominion a Ibadan jihar Oyo

3. Jami’ar Trinity a jihar Ogun

4. Jami’ar Westland a Iwo jihar Osun

A lissafe adadin jami’o’i masu zaman kan su a kasar ya kai 79 kenan.

Kafin amincewa da sabbin jami’oi hudu da aka yi yau, Najeriya na da jami’o’i mallakar gwamnatin tarayya 40 ne, Jami’o’i mallakar gwamnatocin jihohi 45 da masu zaman kansu 75.

An fara kafa jami’o’i masu zaman kan su a kasar nan ne a 1999 in da aka kirkiro da jami’o’i 3 da suka hada da jami’o’in Babcock, Igbinedion da Madonna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here