AN YI ARANGAMA TSAKANIN \’YAN APC DA PDP A ILORIN

  0
  658

  Daga Usman Nasidi 

  A RANAR Lahadi, ne mambobin jam\’iyyar APC da na PDP suka yi wani kazamin rikici a unguwannin Ode Alfa, Agbaji da Ayelabegan dake cikin garin Ilorin, babban birnin jihar Kwara.

  Majiyarmu ta samu labarin cewar mutane da dama sun samu raunuka sakamakon harbe-harben bindiga tsakanin masu rikicin.

  Rahotanni sun bayyana cewar \’yan dabar siyasar sun lalata ababen hawan jama\’a, yayinda mambobin jam\’iyyun suka gudu domin neman mafaka.

  Da yake tabbatar da barkewar rikicin, kakakin rundunar \’yan sanda a jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya ce suna gudanar da bincike domin tabbatar da sun kama masu hannu a cikin tashin hankalin da ya afku.

  Kazalika ya kira ga masu tayar da hankalin jama\’a da shugabannin jam\’iyyu a kan yiwa masoya da magoya bayansu gargadi, yana mai bayyana cewar rundunar \’yan sanda zata saka kafar wando daya da duk wanda ta kama da laifin tayar da tsugune tsaye.

  Wani jawabi da Rafiu Ajakaye, kakakin dan takarar gwamnan jihar ta Kwara a karkashin jam\’iyyar APC, ya fitar, ya ce wasu mutane biyu da suka samu munanan raunuka na samun kulawa a asibiti.

  Wani mamba a jam\’iyyar PDP, Baba Idris, ya ce wasu mutane biyu da aka harba sun mutu daga baya, sannan ya kara da cewa a kalla motoci 20 ne aka lalata.

  Rikicin ya barke ne yayin yakin neman zaben dan takarar APC, AbdulRahman AbdulRazak, lamarin da yasa jami\’an tsaro gaggauta dauke shi daga wurin taron.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here